Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Ibrahim Idris

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar bakin cikinsa game da rasuwar tsohon gwamnan jihar Kogi Alhaji Ibrahim Idris yana da shekaru 77 a duniya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mista Bayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin Shugaba Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin gwamnatin jihar Kogi da al’ummarta tare da abokansa abokan aikinsa da kuma takwarorinsa a fagen siyasa.
Shugaban ya bayyana rasuwar tsohon gwamnan a matsayin babban rashi ga jihar Kogi da Najeriya baki daya inda ya lura cewa “tsohon gwamnan ya sadaukar da babban bangare na rayuwarsa wajen yi wa jama’a hidima da kuma bunkasa jiharsa.”
Shugaba Tinubu ya yaba da gudummawar da ya bayar wajen ci gaban dimokuradiyyar Najeriya da kuma tsawon shekarun da ya shafe yana gudanar da harkokin jama’a.
Shugaban ya ce “Alhaji Ibrahim Idris ya kasance mai sadaukarwa wajen yi wa jama’a hidima kuma shekarun da ya yi a kan karagar mulki sun zama muhimmin babi a tarihin siyasa da ci gaban jihar Kogi.
“Rasuwarsa babban rashi ne mai zafi ga iyalansa jihar Kogi da Najeriya. A wannan lokaci mai wahala dole ne mu tuna tare da girmama gudummawar da ya bayar wajen bunkasa jiharsa da kasarmu.
“Ina mika sakon ta’aziyyata ta musamman ga iyalansa da al’ummar jihar Kogi. Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kurakuransa Ya karbi ayyukansa na kwarai kuma Ya ba shi Aljannah Firdaus.”
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba iyalansa karfin gwiwa da juriyar jure wannan rashi.
Alhaji Idris ya yi aiki a matsayin gwamnan jihar Kogi daga shekarar 2003 zuwa 2011. Gwamnatinsa ta aiwatar da muhimman ayyuka a fannonin samar da ababen more rayuwa ilimi kiwon lafiya da sauran muhimman bangarori.



