Siyasa

APC Ta Tara Magoya Baya 20,000 A Jihar Kwara Domin Zaben 2027

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kwara ta kara kaimi wajen hada kan jama’a a matakin tushe gabanin babban zaben shekarar 2027 inda ta gudanar da wani babban taro a Ilorin domin neman goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da dan takarar gwamna na jam’iyyar Salihu Yakubu Danladi.

Taron wanda masu shirya shi suka bayyana a matsayin gangamin mutane 20,000 ya samu halartar mambobin jam’iyyar da magoya baya daga kananan hukumomin Ilorin West Ilorin East Ilorin South Asa da Moro.

Taron wanda ya samu shirya-shirya daga hannun Mashawarcin Gwamna na Musamman kan Harkokin Siyasa Suleiman Abubakar Sai Kayi an yi shi ne domin nuna goyon baya ga shugabancin jam’iyyar APC da kuma ‘yan takararta.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Gangamin Jam’iyyar APC A Jihar Kwara

Jerin gwano ya fara ne daga mahadar hanya ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (wato Babban Asibiti) sannan ya ratsa manyan titunan birnin Ilorin yayin da mahalarta suka nuna launukan jam’iyyar tare da rera wakokin nuna goyon baya.

Mabiya da dama sun sanya kayan jam’iyyar APC da huluna dauke da rubuce-rubuce irin su ‘Kuri’ata ta APC ce’ da kuma ‘Iwaju LaNlo’.

Da yake magana da manema labarai Sai Kayi ya bayyana cewa an shirya gangamin ne domin nuna godiya kan ayyukan da AbdulRazaq ya gudanar a fannonin samar da ababen more rayuwa ilimi da kuma kula da walwalar ma’aikata da masu karbar fansho.

Ya bayyana fitowar Danladi a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a matsayin wani shiri na ci gaba da ayyukan da aka fara, wanda ya ginu a kan adalci da daidaito. Ya nuna kwarin gwiwar cewa gwamnatin da ke shigowa za ta karfafa tare da dore da nasarorin da gwamnatin mai ci ta samu.

“Matasa ne suka fi yawa a cikin wannan taro idan aka kwatanta su da sauran shekarun mutane. Mun taru ne domin nuna godiya ga Malam AbdulRahman AbdulRazaq bisa ba mu SYD. SYD tana cikin mazabarmu” in ji shi.

Sai Kayi ya kara da cewa jam’iyyar APC ta kuduri aniyar ci gaba da tafiyar da ayyukan ci gaba a kan gudun da ake yi a yanzu inda ya lura cewa Danladi ya kasance cikin wadanda suka taimaka wajen samun nasarorin da gwamnatin AbdulRazaq ta samu tun shekarar 2019.

A nasa jawabin Babban Mai Ba Gwamna Shawara Sa’adu Salahu ya yi kira ga masu zabe da su tantance ‘yan takara bisa la’akari da ayyukan da suka yi a baya da gudunmawar da suka bayar ga al’umma maimakon sauraron kamfen din ‘yan adawa.

Ya bayyana cewa shugabancin AbdulRazaq ya dakile tashin hankalin siyasa tare da inganta zaman lafiya da hakuri inda ya kwatanta salon wannan gwamnati da na gwamnatocin baya.

“Za a iya samun sabani a siyasa, amma za ku yarda da ni cewa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bai taba karfafa amfani da ‘yan daba a siyasa ba sabanin yadda gwamnatin baya ta yi” in ji shi.

Haka kuma Salahu ya yi watsi da yiwuwar cewa wata kawancen jam’iyyu daban-daban za ta iya samun karbuwa a jihar Kwara inda ya nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben 2027 a fadin jihar.

Ya bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da gudanar da ayyukan tara magoya baya cikin lumana tare da kara kaimi wajen gudanar da kamfen na zuwa gidajen mutane kai tsaye.

Haka zalika Darakta Janar na Majalisar Yakin Neman Zaben jam’iyyar APC (a yankin Kwara ta Tsakiya) Abdulrazaq Jiddah ya yaba wa mambobin jam’iyyar bisa fitowarsu sannan ya yi kira ga masu cancantar kada kuri’a da su je su karbi katunan zabensu na dindindin (PVC) da zarar an fara aikin rarraba su.

Babban Manajan Shirin Zuba Jari na Zamantakewa na Jihar Kwara Dr. Abdulwasiu Tejidini ya bayyana cewa fitowar maza mata da matasa na nuni da karuwar goyon baya ga jam’iyyar APC da kuma tsare-tsarenta na ci gaba.

“A yau yankin Kwara ta Tsakiya ya yi magana. Dukkan jihar Kwara ta yi magana domin ayyukan alheri da Mai Girma Gwamnan Jihar Kwara ya gudanar sun yi magana da kansu” in ji shi.

Wani tsohon dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kwara a jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Share Oke-Ode Abdulrasheed Akogun ya bayyana matakin ware tikitin takarar gwamna ga yankin Kwara ta Arewa a matsayin wani babban ci gaba na siyasa mai tarihi ga yankin.

Ya yaba wa Gwamna AbdulRazaq bisa inganta daidaito adalci da gaskiya inda ya kara da cewa gwamnan ya samar da fili mai cike da daidaito ga dukkan mambobin jam’iyyar yayin zaben fidda gwani ba tare da la’akari da bangaren siyasar da suke ciki ba.

Daga cikin sauran manyan mutanen da suka halarci taron akwai Sa’adat Yakubu Danladi matar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara ‘yan majalisa da ‘yan takara Fatima Arinola Lawal da Mariam Yusuf Aladi Dr. Ghali Alaya Mashawarcin Musamman ga Gwamna kan Harkokin Yada Labarai Bashir Adigun shugabannin kananan hukumomin da suka halarci taron da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar APC.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button