Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Jagoranci Tawagar Najeriya Zuwa Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo Na 81

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya tashi daga Najeriya domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Dinkin Duniya na Babban Zaure (UNGA) karo na 81 a birnin New York na kasar Amurka.
Mataimakin Shugaban Kasa Shettima zai jagoranci tawagar manyan jami’ai da suka hada da Gwamnoni Siminalayi Fubara na Jihar Rivers da Dauda Lawal na Jihar Zamfara tare da Ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati.
Za a gudanar da babban taron muhawara na UNGA karo na 81 daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Satumbar 2026 karkashin taken “Farfado da amincewa da kuma tafiyar da sauye-sauye Majalisar Dinkin Duniya mai samar da sakamako ga kowa.”

KARANTA KUMA:http://Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS
A wajen Muhawarar Mataimakin Shugaban Kasa Shettima zai gabatar da sanarwar kasa ta Najeriya inda zai bayyana matsayin kasar da kuma abubuwan da suka fi daukar hankali kan manyan batutuwan duniya tare da tasirinsu ga ci gaban kasa zaman lafiya da tsaro ci gaban tattalin arziki da hadin gwiwar kasa da kasa.
Mataimakin Shugaban Kasa zai kuma halarci manyan taruka a lokacin makon UNGA ciki har da tattaunawa kan ‘Yancin Ci Gaba daukar matakin yanayi da sauran batutuwan da suka shafi dabarun Najeriya da nahiyar Afirka.
Ana kuma sa ran Mataimakin Shugaban Kasa zai hadu da sauran shugabannin duniya a liyafar gargajiya ta Shugabannin Wakilai tare da halartar jerin tarurrukan hadin gwiwa da shugabannin wasu kasashe kungiyoyi na kasa da kasa da abokan huldar ci gaba a gefen Babban Taron.
Taro zai bai wa Najeriya damar ci gaba da diflomasiyyar tattalin arziki ta Shugaba Tinubu zurfafa kawancen dabaru da kuma karfafa muryar kasar kan gyaran tsarin kudi na duniya ci gaba mai dorewa harkokin kudi na yanayi da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban.
Mataimakin Shugaban Kasa Shettima zai dawo Najeriya bayan kammala ayyukansa a New York.



