Hadarin Jirgin Ruwa: Shugaba Tinubu Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Gangamin Siyasa A Ibadan Cikin Yanayi Na Takaitawa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gudanar da taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 21 ga Nuwamba a Ibadan jihar Oyo ba tare da shagulgulan murna ba domin girmama wadanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su ranar Juma’a a karamar hukumar Ijaw ta Kudu da ke jihar Bayelsa.
Jirgin ruwan wanda ke dauke da masu makoki zuwa jana’iza ya kife a mahadar kogi tsakanin al’ummomin Oweikorogha da Otuan a karamar hukumar Ijaw ta Kudu da ke jihar Bayelsa.
Shugaba Tinubu a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan labarai da dabaru Bayo Onanuga ya fitar ya bayyana matukar bakin ciki game da wannan bala’i.
Shugaban ya bayyana mutuwar a matsayin “abin tausayi da takaici” yana umurtar dukkan hukumomin da suka dace da su hada kai wajen tabbatar da ayyukan ceto da murmurewa.
Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan da suka rasu gwamnati da mutanen jihar Bayelsa musamman Gwamna Duoye Diri.
Ya kara da bayyana cewa shawarar gudanar da taron yakin neman zaben na Ibadan ba tare da wani gagarumin biki ba “Alama ce ta girmamawa ga mamatan da kuma hadin kai ga iyalan da bala’in ya shafa.”
“Waɗanda suka rasa rayukansu a cikin wannan bala’i ba su cancanci mutuwa ta wannan hanyar ba. Na umarci dukkan hukumomin da abin ya shafa na Tarayya da su yi aiki tare don tabbatar da nasarar aikin murmurewa da ceto.
“Na kuma ba da umarnin a yi taron yakin neman zaben shugaban ƙasa da za a yi a Ibadan Jihar Oyo a wannan Asabar 21 ga Nuwamba 2026 ba tare da wani gagarumin biki ba don girmama rayukan da aka rasa da kuma tausayawa ga dangi da iyalan waɗanda suka shiga cikin bala’in” cewar Shugaban.
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ba wa waɗanda suka mutu hutu na har abada tare da ta’aziyya ga iyalansu da ke cikin makoki.



