Kungiyar Golden Eaglets Ta Najeriya Ta Fice Daga Gasar WAFU-B Ta ‘Yan Kasa Da Shekaru17

Kungiyar kwallon kafa ta matasan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 17 wato Golden Eaglets ta yi bankwana da gasar WAFU-B ta wannan shekarar da ake gudanarwa a kasar Burkina Faso bayan ta tashi kunnen doki 1-1 da kasar Cote d’Ivoire a wasansu na karshe a matakin rukuni ranar Asabar.
Rashin nasarar da suka yi da ci 1-2 a hannun Jamhuriyar Nijar ranar Laraba ya sanya wasan na ranar Asabar da tawagar Cote d’Ivoire ya zama dole su yi nasara a ciki sai dai Golden Eaglets din ne suka fara shiga matsala bayan Alex Fousseni ya yi amfani da damar kai hari ba-zata inda ya sanya tawagarsa ta jagoranci wasan a minti na 16.
Golden Eaglets sun ci gaba da kai hare-hare masu karfi amma sun kasa samun hanyar zura kwallo a ragar abokan karawarsu har sai da Abiodun John ya samu nasarar dawo da wasan kunnen doki a lokacin da ya rage saura minti biyu kacal a kammala wasan.
Wannan sakamakon ya nuna cewa Golden Eaglets sun fita daga gasar WAFU-B ta ‘yan kasa da shekaru 17 tun a matakin rukuni.
Haka kuma sakamakon ya kawo karshen burin Golden Eaglets na shiga gasar cin kofin Afirka na ‘yan kasa da shekaru 17 da kuma gasar cin kofin duniya na FIFA na ‘yan kasa da shekaru 17 inda gasar ta Afirka ke zama matakin neman tikitin shiga gasar ta duniya.
Golden Eaglets sun taba lashe gasar cin kofin duniya sau biyar amma ba su halarci gasar ba tun shekarar 2019. Sun kammala a matsayin na karshe a Rukuni na B, inda suka samu maki daya kacal daga wasanni biyu.
A daya bangaren Cote d’Ivoire ta kammala a matsayi na biyu da maki biyu yayin da Nijar ta jagoranci rukunin da maki hudu.



