
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta ceto mutane 75 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su kusa da Birnin Gwari a jihar.
Mutanen wadanda suka hada da maza mata da yara ‘yan kabilar Fulani suna tafiya ne a cikin motocin haya lokacin da ‘yan bindiga dauke da bindigogin AK-47 da sauran makamai masu karfi suka tare su a kauyen Folwaya kusa da Birnin Gwari a ranar 19 ga watan Agusta, 2026.
A cewar rundunar ‘yan sandan an sanar da su game da lamarin da misalin karfe 5:30 na yamma ta hannun kungiyar direbobi da ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) reshen Birnin Gwari.
Bayan samun rahoton an tura wata kwararriyar tawagar ‘yan sanda daga sashen Birnin Gwari zuwa wurin nan take.
An bayyana cewa masu garkuwar sun kai wadanda suka sace din cikin daji tare da boye su a wani kogo da ke cikin tsaunuka.
Sai dai ‘yan bindigar sun tsere bayan sun hango jami’an ‘yan sandan da ke dauke da makamai masu karfi inda suka bar wadanda suka yi garkuwa da su a wurin.
Daga bisani aka ceto mutanen 75 din ba tare da sun samu wani rauni ba.
KARANTA KUMA: Sanatocin Arewa Sun Yi Kira da a Hanzarta Kafa ‘Yan Sandan Jiha
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna CP Rabiu Muhammad ya yaba wa kungiyar NURTW reshen Birnin Gwari bisa samar da muhimman bayanai a kan lokaci wadanda suka taimaka wajen nasarar aikin ceto mutanen.
Ya kuma yaba wa Kwamandan ‘Yan Sanda na yankin Birnin Gwari da jami’ansa bisa daukar mataki cikin gaggawa da kwarewa.
Kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da kasancewa cikin shiri da kuma sanar da ‘yan sanda duk wani motsi ko aiki na shakku ba tare da bata lokaci ba.
Ya kuma gargadi jama’a game da daukar doka a hannunsu inda ya yi nuni da cewa irin wadannan ayyuka na iya haifar da asarar rayukan marasa laifi.
Safina Umar Farouk.



