Najeriya

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Yi Kira Ga Musulmai Su Yi Koyi Da Halayen Manzon Allah

Safina Umar Farouk

Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta yi kira ga ‘yan kasa musamman ma Musulmi yayin da suke bikin Maulidin Annabi da su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammadu.

Ta yi wannan kiran ne a cikin sakon da ta fitar domin tunawa da ranar haihuwar Annabin.

Har ila yau Mrs. Tinubu ta yi addu’ar samun hadin kai da zaman lafiya mai dorewa a dukkan sassan kasar nan.

KARANTA KUMA: Maulidi: Uwargida ta yi kira da a kara nuna kauna a tsakanin ‘yan Najeriya

Ta ce: “Yayin da muke bikin Maulidin Annabi na shekarar 2026 ina mika sakon gaisuwa mai cike da kauna ga dukkan Musulmi a fadin Najeriya.

“Bikin tunawa da haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) yana tunatar da mu rayuwarsa ta misali da kuma kyawawan halayensa masu dorewa na tausayi gafara da kuma zaman lafiya tare.

“Ina karfafa gwiwar dukkan Musulmi da su yi koyi da wadannan kyawawan halaye tare da ci gaba da inganta zaman lafiya a gidajenmu al’ummominmu da kuma kasarmu baki daya.

“Allah ya sa wannan biki ya karfafa dankon zumunci da hadin kai a tsakaninmu tare da kawo sabon fata zaman lafiya da albarka ga dukkan ‘yan Najeriya.

“Barka da bikin Maulidin Annabi na 2026!”

 

Safina Umar Farouk.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button