Afirka

Shugaban Kasar Chadi Ya Yi Wa Shugaban ‘Yan Adawa Afuwa

Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Déby ya yi wa tsohon Firayim Minista kuma shugaban ‘yan adawa Succès Masra afuwa matakin da ya kawo karshen hukuncin daurin shekaru 20 da aka yanke masa tare da ba shi damar samun ‘yanci.

An sanar da wannan afuwa ne ta hanyar dokar shugaban kasa a ranar Juma’a inda aka yi watsi da hukuncin daurin kurkuku gaba daya ga wadanda dokar ta shafa.

Masra wanda shi ne shugaban babban jam’iyyar adawa ta kasar Chadi yana fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 ne bayan an same shi da laifi matakin da magoya bayan ‘yan adawa da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka soki tare da bayyana shi a matsayin wanda ke da nasaba da siyasa.

Tsohon Firayim Ministan ya kasance daya daga cikin manyan masu sukar gwamnatin Déby da kuma muhimmin mutum a fagen siyasar ‘yan adawa a kasar Chadi.

Fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilan wannan afuwa ba lamarin da ya haifar da shakku kan ko sakin Masra zai iya haifar da sabon tattaunawar siyasa tsakanin gwamnati da ‘yan adawa.

 

Africanews/LADAN NASIDI.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button