Shugaba Tinubu ya karɓi Babban Kwamishinan Birtaniya Mai shirin Barin Mukaminsa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin Babban Kwamishinan Birtaniya mai barin gado a Najeriya Dr. Richard Montgomery (CMG) a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Alhamis.
Wannan ganawa ta kasance wani bangare na ayyukan Babban Kwamishinan yayin da yake kammala aikinsa na diflomasiyya a Najeriya.
Dr. Montgomery ya yi aiki a matsayin Babban Kwamishinan Birtaniya a Najeriya inda ya kula da harkokin diflomasiyya da dangantaka tsakanin kasashen biyu a tsawon lokacin da ya shafe yana rike da mukamin.
KARANTA KUMA: Birtaniya ta nada sabon Mataimakin Babban Kwamishina a Najeriya
Haka kuma ganawar ta ba Shugaba Tinubu da jakadan mai barin gado damar tattaunawa kan kammala wa’adin aikinsa a Najeriya.
LADAN NASIDI.



