Uncategorized

Shugaba Tinubu ya yaba da nasarar ceto mambobin NYSC 15

Shugaba Bola Tinubu ya yi maraba da kubutar da mambobi 15 na shirin bautar kasa (NYSC) da wasu ‘yan Najeriya shida da ‘yan ta’adda suka sace a jihar Kogi a makon da ya gabata.

 

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X (@OfficialABAT) ranar Litinin Shugaba Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda dukkan mutane 21 da aka sace—wadanda suka hada da maza takwas da mata 13—suka samu ‘yancinsu bayan wani aiki na hadin gwiwa na neman da kuma kubutar da su.

 

Ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne ta hanyar hadin gwiwar jami’an soji da ‘yan sandan Najeriya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kuma ‘yan sa-kai na yankin a cikin dazukan karamar hukumar Ofu ta jihar Kogi.

 

KARANTA KUMA: Sojoji sun kubutar da wadanda aka sace sun ci gaba da farmakar ‘yan ta’adda a Kogi

Shugaban ya ce a yanzu ana ba wadanda aka kubutar din kulawar likita kafin a sake hada su da iyalansu.

 

Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro na ci gaba da farautar masu garkuwar biyo bayan umarninsa na ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka a fadin kasar.

 

“Za a hukunta wadanda ke da hannu a lamarin yadda doka ta tanada da kuma hukumomin tsaronmu za su bi sahun duk wanda ya taimaka wajen aikata wannan laifi” in ji shi.

Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da cewa ‘yan Najeriya za su iya tafiye-tafiye a fadin kasar ba tare da fargaba ba tare da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

 

 

Ladan Nasidi.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button