
Gwamnan Jihar Taraba Agbu Kefas ya yi alkawarin ba Shugaba Bola Tinubu cikakken goyon baya gabanin zaben shekarar 2027 inda ya bayyana cewa jihar Taraba tana tare da jam’iyyar APC dari bisa dari.
Gwamna Kefas ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja inda ya ce matakan da gwamnatin tarayya ke dauka a fannonin tsaro ilimi kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa suna haifar da sakamako mai kyau da ake gani a fadin jihar Taraba.
Gwamnan, wanda shi ne kuma shugaban jam’iyyar APC a jihar ya ce ziyarar tasa ta zo ne domin tarbar Shugaban kasa bayan dawowarsa da kuma mika ta’aziyya kan hatsarin jirgin saman Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ya faru kwanan nan a jihar Ondo.
Ya bayyana hatsarin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an soji da sauran ‘yan kasa a matsayin babban al’amari mai tada hankali ga kasa baki daya wanda ya cancanci a nuna jimami tare.
KARANTA KUMA:http://Shugabannin Yankin Arewacin Kwara Sun Goyon Bayan Shirin Sake Zaben Shugaba Tinubu
“Ni ne kuma shugaban jam’iyya a jihata don haka na zo ne domin tarbar Shugaban kasa bayan dawowarsa m tare da mika ta’aziyya kan hatsarin jirgin saman Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da kuma rashin jami’ai da ‘yan kasar da suka rasa rayukansu a hatsarin” in ji Kefas.
Baya ga ziyarar ta’aziyyar gwamnan ya yaba da tasirin ayyukan gwamnatin Tinubu a jihar Taraba inda ya ce mazauna jihar suna cin moriyar tallafin gwamnatin tarayya kai tsaye a muhimman fannoni.
Kara Karfafa Goyon Bayan Jama’a
A cewarsa inganta tsaro ilimi kyauta ayyukan kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa sun kara karfafa amincewar jama’a ga gwamnatin Najeriya tare da kara karfafa goyon bayansu ga Shugaban kasa.
“Kuna iya ganin cewa ina kasa ina sa ido muna tafiyar da al’amura yadda ya kamata. Jama’a suna jin dadin dukkan matakan da tallafin da Shugaban kasa ke bayarwa tun daga fannin tsaro ilimi kyauta tsarin kiwon lafiya har zuwa samar da ababen more rayuwa” in ji shi.
Kefas ya ce fa’idodin shirye-shiryen gwamnatin Najeriya sun kara karfafa amincewar jama’a ga Shugaba Tinubu tare da karfafa kudirinsu na ci gaba da goyon bayansa a zaben shugaban kasa mai zuwa.
“Don haka mutanen ba su da wata shakka kuma sun samu cikakken tabbacin cewa Shugaban kasa na tuntubarsu ta hannuna saboda haka za su zabi Shugaban kasa” in ji shi.
Sakamakon haka Gwamnan ya ayyana cewa Jihar Taraba jiha ce ta jam’iyyar APC dari bisa dari.



