NajeriyaNishadi.

Shugaba Tinubu Ya Taya Dansa Murnar Samun Sarauta Ya Bukaci Ya Yi Wa Al’umma Hidima

Shugaba Bola Tinubu ya taya dansa Seyi Tinubu murnar nada shi sarautar ‘Dan Zaki Gwandu’ a Jihar Kebbi inda ya bukace shi da ya gudanar da nauyin da ke tattare da sabon mukamin nasa na gargajiya cikin tawali’u jarumtaka da sadaukarwa wajen hidima.

Shugaban ya jaddada cewa wannan karramawa ta wuce batun samun daukaka ta kashin kai kawai ya bayyana ta a matsayin kira na dorewa kan dabi’un shugabanci inganta zaman lafiya da fahimtar juna da kuma bayar da gudummawa ga jin dadin al’umma.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon taya murna da aka fitar a ranar Laraba wanda kuma ya samu sanya hannun Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru Mista Bayo Onanuga biyo bayan nada dansa a wannan sarauta ta gargajiya.

KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Taya Gwamnan Kwara Murnar Samun Sarauta a Ilorin

Shugaban ya nuna godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Gwandu da Majalisar Masarautar Gwandu bisa wannan karramawa wadda sarkin ya bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin masarautar.

“A matsayina na uba na ji dadin ganin an karrama dana ta hanyar wata cibiyar gargajiya mai tarihi mai cike da daukaka.

“Sai dai kuma ina tunatar da shi cewa duk wata karramawa tana zuwa ne tare da nauyi. Sarautar ‘Dan Zaki Gwandu’ tana kunshe da dabi’un jarumtaka shugabanci da kuma hidima.” Ina kira gare shi da ya yi rayuwa bisa ga wadannan dabi’u ya kasance mai tawali’u kuma ya ci gaba da sadaukar da kansa domin amfanin sauran mutane” in ji Shugaban kasa.

Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da dansa ya bayar wajen shigar da matasa harkoki ci gaban al’umma da karfafa su musamman ta hanyar rawar da ya taka a kungiyar ‘City Boy Movement’ da sauran shirye-shiryen da ke tallafawa matasan Najeriya.

Ya bukaci Seyi Tinubu da ya dauki wannan lakabi a matsayin kira na kara kaimi wajen bunkasa matasa inganta zaman lafiya da kuma hidimtawa kasar Najeriya.

Shugaban ya kara da cewa wannan karramawa tana nuna karfin dangantakar abota girmama juna da hadin kai da ke tsakanin al’ummomin Najeriya daban-daban.

Ya sake jaddada muhimmancin masarautun gargajiya a matsayin masu kula da tarihi al’adu da hadin kan kasa tare da mika godiya ga Sarkin Gwandu da al’ummar jihar Kebbi bisa karrama dansa da suka yi.

Shugaba Tinubu ya yi wa Seyi Tinubu fatan samun hikima tawali’u da karfin gwiwa yayin da yake karbar nauyin da ke tattare da sabon lakabin sarautar gargajiyar da aka ba shi.

Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ne ya nada Seyi Tinubu a matsayin ‘Dan Zaki Gwandu’ wato ‘Dan Zakin Gwandu’  a fadar tarihi ta Abdullahi Fodiyo da ke Birnin Kebbi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button