Najeriya

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Za Tashi Zuwa Kasar Saliyo Don Taron kolin ECOWAS Karo Na 69

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya tashi daga Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 69 a birnin Freetown na kasar Saliyo.

Zai gana da sauran shugabannin siyasa da na bangaren kasuwanci daga sassan Yammacin Afirka da ma wuraren da suka wuce haka a wajen taron, wanda aka shirya gudanarwa a Cibiyar Taro ta Duniya ta Julius Maada Bio da ke Freetown a yau, 19 ga watan Yulin 2026.

KARANTA KUMA: Najeriya ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin

Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan muhimman shawarwari na manufofi da kudirori masu zurfi, tare da sake jaddada kudirin shugabannin na bai-daya game da zaman lafiya, dimokuradiyya, ci gaban tattalin arziki, da kuma hadin gwiwar kasashen yankin.

Wannan taron wani bangare ne na tarukan doka na tsakiyar shekara na kungiyar ECOWAS, wadanda ke hada shugabannin kasashe da na gwamnatoci, ministoci, manyan jami’ai da hukumomin yankin domin ciyar da manufofin kungiyar gaba—wadanda suka hada da tsaro, tafiyar da mulki bisa tsarin dimokuradiyya, hadewar tattalin arziki, kasuwanci, ababen more rayuwa da ci gaba mai dorewa.

Mataimakin Shugaban Kasa zai dawo Abuja bayan kammala ayyukansa a wannan kasa ta Yammacin Afirka.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button