An zabi Badejo-Sharing A Matsayin Shugaban NBA

An zabi Oyinkansola Badejo-Okusanya, wacce ke rike da mukamin Babban Lauyan Najeriya (SAN), a matsayin Shugabar Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), bayan ta samu kuri’u 12,001 (kashi 47.06%) tare da kayar da wasu ‘yan takara biyu a zaben shugabancin kungiyar.
Sakamakon hukuma ya nuna cewa Lateef Omoyemi Akangbe (SAN) ya samu kuri’u 7,737 (kashi 30.34%), yayin da Olumuyiwa Akinboro (SAN) ya samu kuri’u 5,766 (kashi 22.61%), daga cikin jimillar kuri’u 25,504 da aka kada.
Da take mayar da martani kan zabin nata, Badejo-Okusanya ta gode wa mambobin kungiyar, inda ta ce: “A yau, ina jin cike da matukar godiya da kuma nauyin da ke kaina. Na gode wa mambobin Kungiyar Lauyoyin Najeriya bisa amincewar da kuka nuna mini ta hanyar zabina a matsayin shugabarku. Na ji matukar alfahari da kuma godiya bisa amincewar da kuka nuna.”
Yayin da ta bayyana sakamakon a matsayin nasara ta kowa, ta ce “Wannan nasara ta dukkanmu ce masu imani da kungiyar lauyoyi mai karfin gaske da kuma inganci ga kowa.”
Ta kuma nuna godiya ga sauran ‘yan takarar, tawagar yakin neman zabenta, magoya bayanta, iyalanta, da kuma masu ba ta shawara da jagoranci bisa goyon bayan da suka ba ta a duk tsawon lokacin zaben.
Dangane da makomar kungiyar, zababbar shugabar ta bayyana cewa: “Yakin neman zabe ya kare. Yanzu ne aiki ya fara. Na yi alkawarin yi wa kowane mamba na Kungiyar Lauyoyin Najeriya hidima cikin gaskiya, tawali’u, jaruntaka, da kuma rikon amana. Tare, za mu gina NBA inda lauyoyi za su samu ingantaccen kudin shiga, ingantaccen rayuwa, da kuma ingantaccen yanayin gudanar da aikin lauya. Allah ya albarkaci Kungiyar Lauyoyin Najeriya da kuma Tarayyar Najeriya.”

Da wannan nasara, Badejo-Okusanya, wacce ita kadai ce mace a cikin ‘yan takarar, ta zama shugaba ta 33 ta wannan kungiya mai daraja ta kwararrun lauyoyi a Najeriya.
Aisha.Yahaya, Lagos



