Sall Na Neman Goyon Bayan Senegal Kan Yunƙurinsa Na Samun Matsayi A Majalisar Dinkin Duniya.

Tsohon shugaban kasar Senegal, Macky Sall, ya gana da Shugaba Bassirou Diomaye Faye a Dakar domin neman goyon bayan Senegal kan takararsa ta neman mukamin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya; wannan shi ne karon farko da ya ziyarci kasar tun bayan barin mukaminsa a watan Afrilun 2024.
A cewar fadar shugaban kasar Senegal, Sall ya yi wa Shugaba Faye bayani game da yakin neman zabensa na wannan babban mukami na Majalisar Dinkin Duniya, tare da yin alkawarin ci gaba da sanar da shugaban kasar duk wani ci gaba yayin tsarin zaben. Kasar Burundi, wacce a yanzu take rike da shugabancin kungiyar Tarayyar Afirka (AU) na karba-karba, ita ce ta tsayar da Sall takarar mukamin a farkon wannan shekara.
Dubban magoya baya ne suka tarbi tsohon shugaban kasar a filin jirgin saman soji da ke Dakar, inda ya yi jawabi ga taron jama’ar kafin ya wuce zuwa wurin ganawar da shugaban kasar.
KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban Senegal na Neman Goyon Baya kan Takarar Majalisar Dinkin Duniya
Sall, wanda ya rike mukamin shugaban kasar Senegal daga shekarar 2012 zuwa 2024 kuma ya zauna a kasar Morocco tun bayan barin mukaminsa, ya bar Dakar daga bisani a wannan rana.
Sai dai ziyarar ta jawo suka daga bangarori daban-daban na jam’iyya mai mulki da kuma kungiyoyin farar hula. Masu sukar sun zargi gwamnatin Sall da aiwatar da matakan danniya na siyasa wadanda ake zargin sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a shekarunsa na karshe kan karagar mulki, tare da boye bayanan tattalin arziki marasa dadi.
Ganawar ta kuma bayyana rarrabuwar kawuna a cikin bangaren siyasar Shugaba Faye, biyo bayan matakin da ya dauka na korar tsohon Firayim Minista Ousmane Sonko daga mukaminsa kwanan nan.
A matsayin nuna rashin amincewa da ziyarar ta Sall, daya daga cikin masu ba Shugaba Faye shawara kan harkokin siyasa, Alioune Ibnou Abitalib Sow, ya sanar da murabus dinsa, inda ya bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin wanda ke da alhakin yawancin kalubalen da kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Wata kungiyar hadin gwiwa ta farar hula, wacce ta dade tana sukar matakan danniya a lokacin mulkin Sall, ita ma ta soki ziyarar, tare da sake yin kira a nemi daukar matakin lissafi kan mutuwar mutanen da aka samu a lokacin mulkinsa.
Africanews/Aisha.Yahaya, Lagos



