Fitattun Labarai

Eid al-Maulud: Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Wa Najeriya Addu’a

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga shugabannin addini da su yi amfani da bikin Maulidin Annabi na wannan shekara wajen yi wa Najeriya addu’a tare da karfafa gwiwar mabiyansu wajen nuna kyakkyawan sadaukarwa ga kasa bisa koyarwar Annabi Muhammadu (SAW).

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunshi  Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu a ranar Talata Shugaba Tinubu ya kuma yi kira a yi addu’o’in neman tsari daga matsalar rashin tsaro da sauran kalubalen da ke addabar wasu sassan kasar.

 

KARANTA KUMA: Eid al-Adha: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi kira ga hadin kai da addu’o’i ga Najeriya

Yayin da yake taya Musulmai murnar bikin Maulidi Shugaban ya bukaci mabiya addinin su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu tare da yin amfani da wannan lokaci wajen duba kai yin addu’a da kuma yin nazari kan kyawawan halaye na musamman da Annabin ya mallaka.

“Ya kamata Musulmai su yi kokari na gangan wajen bin koyarwar Annabi Muhammadu. Akwai muhimman darussa na sadaukarwa da juriya da hakuri da  tawali’u da rashin son kai da dukkanmu za mu iya koyo daga rayuwar Annabi” in ji shi.

Shugaban ya bukaci Musulmin da ke bikin Maulidin su nuna kulawa da taimako ga mabukata da kuma masu rauni domin nuna ruhin wannan lokaci mai albarka.

 

 

Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button