Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Isa Paris

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Paris na kasar Faransa domin gudanar da kashi na biyu na hutunsa na aiki na tsawon makonni uku a nahiyar Turai.

Jakadan Najeriya a kasar Faransa Emmanuel Ayodele Oke ne ya tarbi Shugaban a lokacin da ya isa.

Shugaba Tinubu ya bar Abuja kimanin makonni biyu da suka gabata domin fara hutunsa na shekara-shekara inda ya fara da ziyartar birnin London a kasar Birtaniya.

Tun da farko Babban Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru Mista Bayo Onanuga ne ya sanar da batun hutun aikin tare da bayyana jerin wuraren da Shugaban zai ziyarta a cikin wata sanarwa.

“Wurinsa na farko da zai ziyarta shi ne birnin London a kasar Birtaniya” in ji sanarwar wadda ta kara da cewa daga nan Shugaban zai ci gaba da ziyartar wasu sassan nahiyar Turai.

KARANTA KUMA:http://Shugaba Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa Turai domin hutun aiki.

Saboda haka isowar Shugaba Tinubu birnin Paris na nuna ci gaba da hutun aiki na makonni uku da aka tsara.

Mista Onanuga ya kuma bayyana cewa Shugaban zai dawo Najeriya bayan kammala hutun domin shiga shirye-shiryen zaben watan Janairun 2027.

Ana sa ran shugaban na Najeriya zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na hukuma a karshen mako mai zuwa bayan kammala hutunsa na makonni uku.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button