NajeriyaSiyasa

2027: INEC Ta Fitar Da Jerin Sunayen ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa 18 da mataimakansu na zaben gama-gari na shekarar 2027.

A cikin sanarwar da Sakatariyar Hukumar, Rose Anthony, ta sanya wa hannu, an bayyana cewa daga cikin ‘yan takarar 18, maza ne 16 yayin da mata biyu ne kawai.

Jerin ya kunshi ‘yan takarar shugaban kasa 18 da mataimakansu daga jam’iyyun siyasa daban-daban kuma Sakatariyar INEC Rose Oriaran-Anthony ce ta sanya hannu a kai.

Daga cikin wadanda ke kan jerin akwai Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) Gwamnan Jihar Oyo Oluseyi Makinde na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) Sandy Ojang Onor na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kuma tsohon Gwamnan Jihar Cross River Donald Duke na jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP).

KARANTA KUMA: http://NEC ta fitar da tsarin sa ido kan zabe kai-tsaye gabanin zaben gama-gari

Sauran ‘yan takarar shugaban kasa sun hada da Rufai Adekunle Omo-Aje na jam’iyyar Action Alliance (AA), Abbas-Bin Aliyu na jam’iyyar Action Democratic Party (ADP), Yusuf Kabiru na jam’iyyar Action Peoples Party (APP), Omoyele Sowore na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Sunday Adenuga na jam’iyyar Boot Party (BP), Adebisi Olusoji na jam’iyyar Democratic Labour Alliance (DLA) Sunday Okereke na jam’iyyar Labour Party (LP) Adewole Adebayo na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) Peter Agada na jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) da kuma Nwanyanwu Daberechukwu na jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP).

Jerin ya kuma kunshi mata biyu masu takarar shugaban kasa, wadanda su ne Ada Elizabeth Frederick Okwori ta jam’iyyar National Democratic Party (NDP) da Nkem Esther Okereke ta jam’iyyar National Rescue Movement (NRM).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button