Shettima Ya Bar Abuja Zuwa Birnin Addis Ababa

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa Addis Ababa Habasha domin jagorantar wani taron musayar ra’ayi tsakanin gwamnati da wanda ya mayar da hankali kan hanzarta samar da abinci mai gina jiki.
Mataimakin Shugaban Kasa zai halarci taron ne bisa gayyatar Mataimakin Firayim Ministan Habasha Temesgen Tiruneh wanda ke fafutukar ganin an samar da tsarin kasar na bunkasa abinci mai gina jiki a kasar.
A matsayinsa na shugaban tawagar Najeriya Mataimakin Shugaban Kasa zai halarci taron farko na ziyarar Shugabancin Abinci Mai Gina Jiki tsakanin Najeriya da Habasha wani dandali da nufin bai wa masu ruwa da tsaki damar raba abubuwan da suka faru na gina wani shiri na tarayya, jiha da kuma na kananan hukumomi kan abinci mai gina jiki.

KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya yi ta’aziyya ga Jihar Neja kan hatsarin da ya rutsa da ma’aikatan hakar ma’adinai
A yayin ziyarar, tawagar ta Najeriya za ta musanya ra’ayoyi da kwarewa da kasar Habasha kan yadda tsarin da gwamnati ke jagoranta zai iya inganta samar da abinci mai gina jiki tare da ziyartar muhimman cibiyoyin da ke aiki wajen inganta samar da irin wannan abinci a fadin kasar.
Wasu daga cikin wuraren da aka tsara ziyarta sun hada da gonar alkama da gonar ayaba a yankin Oromia Cibiyar Horarwa ta ‘Bounty of the Basket’ da kuma ziyarar gidaje a Mojo da kuma kamfanin Jabdu Motors a Bishoftu.

Mataimakin Shugaban Kasar yana tare da Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal da takwaransa na Jihar Jigawa Umar Namadi.
Har ila yau cikin tawagar akwai Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki Atiku Bagudu takwaransa na Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci Abubakar Kyari da Darakta-Janar na Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) Hajiya Zubaida Umar Abubakar.
Mataimakin Shugaban Kasar zai dawo Abuja bayan kammala ayyukansa a Addis Ababa.
Ladan Nasidi.



