2027: Dan Takarar Kujerar Sanata Na Jam’iyyar APGA Ya Karfafa Aikin Hadin Gwiwa Domin Samun Nasara

Dan takarar kujerar Sanata a jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) mai wakiltar yankin Anambra Central Dozie Nwankwo ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su ci gaba da aiki tare a matsayin tawaga, tare da kai sakonnin jam’iyyar zuwa matakin tushe, duba da cewa nasarar jam’iyyar ta dogara ne kan yadda aka tattara mutane a rumfunan zabe daban-daban.
Nwankwo ya yi wannan kiran ne a sakatariyar karamar hukumar Awka South yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zabe na karamar hukumar Awka South domin goyon bayan ‘yan takarar jam’iyyar APGA da ke neman kujeru a Majalisar Dokokin Tarayya a yankin.
Taron ya hada ‘yan takarar jam’iyyar da dama ciki har da Obi Nwankwo (mai neman wakilci a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga yankin Awka North da South) Samuel Nwofor (mai neman wakilci a Majalisar Dokokin Jiha daga mazabar Awka South ‘A’) da takwaransa na mazabar Awka South ‘B’ Pharm Makuochukwu Egbutu da sauransu.

KARANTA KUMA: APGA Ta Sake Tabbatar da Goyon Bayanta Ga Shugaba Tinubu Kafin 2027
Ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na daukar dabaru da kuma karfafa karfin jam’iyyar na lashe zabe don share fagen jagoranci mai ma’ana ga mutanen da suke fatan yi wa hidima.
Nwankwo ya bayyana cikakken kwarin gwiwar cewa ta hanyar hadin kai da kokarin hadin gwiwa da aka gina kan gangamin jama’a jam’iyyar za ta lashe zaben da ke tafe.
Ya bukaci mambobin da aka rantsar da su da su ci gaba da jajircewa da kuma shirye-shiryen yin sadaukarwa da suka dace yana mai tabbatar da kudurinsa na jawo ra’ayin dimokuradiyya da kuma gina al’umma idan aka zabe su a mukami.
Da yake bayyana su a matsayin masu muhimmanci a tafiyar siyasa ya ce “kaddamar da su ya sanya su a sahun gaba a kokarin tattara jama’a yayin da jam’iyyar ke shirin gudanar da babban zabe.”
Ya nuna bukatar zurfafa alaka da jama’a yana mai jaddada cewa yana yin yakin neman zabe da kuma ci gaba da dabarun da nufin lashe zabe ta hanyar hadin gwiwar masu ruwa da tsaki.
A nasa bangaren, wani dan jam’iyyar Obi Nwankwop ya lissafa gudunmawar da ya bayar ga ci gaban jihar a lokacin da yake aikin gwamnati, sannan ya bukaci mambobin da aka rantsar da su mayar da hankali kan hade kai da kuma wayar da kan jama’a domin tabbatar da nasarar zabe.
Ya karfafa wa ‘yan jam’iyyar gwiwa da su ci gaba da nuna kwarin gwiwa, su guji karaya, su yafe wa junansu shakku da kuma amfani da tattaunawa ta cikin gida don warware duk wani korafi.
Aisha.Yahaya, Lagos



