Kasashe Takwas Sun Yi Kira Da A Gudanar Da Zaben Falasdinawa A shekarar 2027

Ministocin harkokin waje daga ƙasashe takwas sun yi kira ga Hukumar Falasɗinu da ta shirya zaɓen ‘yan majalisa da na shugaban ƙasa a kwata na farko na 2027 a cewar wata sanarwa ta haɗin gwiwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta fitar.
Sanarwar wadda ta bayyana matsayin ministocin ta jaddada kiran da suka yi wa Hukumar Falasɗinu da ta gudanar da zaɓen biyu a cikin wa’adin da aka tsara.
Ostiraliya Belgium Kanada Faransa Luxembourg Norway Poland da Birtaniya sun kuma nuna damuwa game da shawarar da Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas ya yanke na dage zaɓen ‘yan majalisa da aka shirya yi a ranar 28 ga Nuwamba da kuma zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara a farkon 2027.
KARANTA KUMA: Najeriya Da Falasɗinu Sun Ƙarfafa Alaƙa Tsakanin Ƙasashe
Abbas ya dage zaɓen ‘yan majalisa a watan Oktoba inda ya sake tsara shi zuwa ranar 11 ga Satumba 2027 sannan ya kira zaɓen shugaban ƙasa a wannan ranar yana mai ambaton matakan Isra’ila da yanayin tsaro a Gaza.
Jami’ar manufofin harkokin waje ta Tarayyar Turai Kaja Kallas ta ce gudanar da zaɓen dimokuraɗiyya a duk faɗin yankin Falasɗinu da aka mamaye “ya daɗe yana jiran lokaci.”
Falasdinawa ba su gudanar da zaɓen ‘yan majalisa ba tun shekarar 2006 ko kuma zaɓen shugaban ƙasa tun shekarar 2005.
Abbas ya yi alƙawari a rubuce ga shugaban Faransa Emmanuel Macron da Yarima Mohammed bin Salman na Saudiyya don gudanar da zaɓen biyu a matsayin wani ɓangare na amincewa da ƙasar Falasɗinawa a watan Satumba na 2025.



