Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Sake Jaddada Goyon Bayan Najeriya Ga Kananan Sana’o’i

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya sake jaddada kudurin Gwamnatin Najeriya na tallafawa kananan sana’o’i, inda ya bayyana su a matsayin ginshikin tattalin arzikin kasar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen taron tattaunawa da aka shirya domin masu kananan sana’o’i da masu sana’ar hannu a Jihar Borno inda ya halarci taron a matsayin babban bako na musamman.
Mataimakin Shugaban Kasar ya yi nuni da cewa an samu gagarumin ci gaba a fannin kananan sana’o’i tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya karbi ragamar mulki a shekarar 2023.

KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Ba da Tabbacin Karin Tallafi ga Kananan Kasuwanci
Ya ce: “A cikin shekaru uku da suka gabata mun zagaya sassan Najeriya daban-daban domin tallafawa kananan kasuwanci. Mun gamsu matuka cewa su ne ginshikin duk wani tsarin tattalin arziki.
“Saboda haka kasuwancinku bai taba zama abu na gefe ba a cikin tsarinmu na tattalin arziki. Ina alfaharin dawowa gida Borno a yau, domin bayar da rahoto kan ci gaban da muka samu” in ji shi.

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bai wa masu kananan sana’o’i tabbacin samun karin tallafi inda ya jaddada cewa tattalin arzikin Najeriya yana kan hanyar samun daukaka sakamakon kyawawan gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar.
“Babu shakka cewa mun tarar da tattalin arziki a gabar rugujewa amma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fuskanci zabuka masu wuyar gaske wadanda ba za a iya ci gaba da dage su ba.
Duk da haka alkaluma da bayanan tarihi ba za su iya bayyana komai ba. “Harshen da talakawa ke fahimta da farko shi ne na tasiri kai tsaye a rayuwarsu shi ya sa muka sanya a gaba a matsayin nauyi a kanmu, mu kawo sauyi na hakika a rayuwarsu ta yau da kullum” in ji shi.

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya bayyana cewa karfafa tattalin arziki ya wuce kawai batun rage talauci inda ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa kananan sana’o’i a matsayin wani muhimmin bangare na tsarin gwamnatinsa na sake gina jihar.
A nasa bangaren Karamin Ministan Masana’antu John Enoh ya yaba da hazaka da juriyar kanana da matsakaitan sana’o’i (MSMEs) wajen samar da ayyukan yi da kuma bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin kasa.

Ya sake jaddada kudurin gwamnatin Tinubu na karfafa kananan sana’o’i da kuma fadada damammaki ga ‘yan kasuwa.
Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan samar da ayyukan yi da kanana da matsakaitan sana’o’i (MSMEs) Mista Temitola Adekunle-Johnson ya bayyana cewa “an shirya taron ne domin tantance ci gaban sana’o’in da suka samu tallafi daga gwamnati.”
Ya bayyana cewa masu kananan sana’o’i 5,000 a Jihar Borno sun ci gajiyar shirye-shiryen tallafi daban-daban na Gwamnatin Tarayya.
Aisha.Yahaya, Lagos



