Najeriya

Aikin Hajji Na 2026: Mahmoud Ya Nemi Taimakon Allah Ga Najeriya

Ministan Jiha na Babban Birnin Tarayya (FCT) Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta yi kira ga Kiristocin Najeriya da za su tafi aikin hajji a shekarar 2026 zuwa ƙasashen Jordan da Isra’ila da su yi addu’ar samun zaman lafiya tsaro haɗin kai da wadata a Najeriya.

Dr. Mariya Mahmoud ta yi wannan kiran ne yayin bikin ƙaddamar da aikin hajji na Kiristoci na shekarar 2026 a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Da take magana kan taken “Aikin Hajji: Alkawarinmu na Dorewa” Ministar ta bayyana aikin hajji a matsayin fiye da tafiya ta ruhaniya kawai ta ce yana ba wa Kiristoci damar sabunta ruhinsu yin tunani mai zurf ƙarfafa imani da kuma sabunta ƙudurin bin koyarwar Yesu Kristi.

A madadin Ministar Babban Sakatare mai kula da Ayyukan Gama-gari a Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) Mista Ajayi Rotimi kya bayyana cewa ziyartar wurare masu tsarki da ke da alaƙa da rayuwa hidima mutuwa da tashin Yesu Kristi zai taimaka wa mahajjatan wajen ƙarfafa alaƙarsu da Allah da kuma sabunta sadaukarwarsu ga dabi’un Kiristanci—kamar ƙauna gafara tawali’u tausayi da hidima ga ɗan adam.

Ta ce taken ya jaddada nauyin da ke kan kowace tsara na kare da haɓaka gadon ruhaniyarsu. Ta nanata cewa imani ba wai kawai abin da ake gado ba ne a’a ya kamata a nuna shi ta hanyar halayen yau da kullum, biyayya sadaukarwa zama lafiya da juna da kuma nuna ƙauna ga kowa.

Ministar ta sake jaddada ƙudurin Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA)—a ƙarƙashin jagorancin Ministan FCT Nyesom Wike—na kare ‘yancin addini da kuma inganta zaman lafiya tsakanin mutanen da ke da akidu daban-daban na addini.

Ta yaba wa hukumomin da ke da alhakin shirya aikin hajjin saboda sadaukarwarsu da tsare-tsarensu na ƙwarai. Haka kuma ta yi kira ga mahajjatan da su nuna mutunci, ladabi, tawali’u, da kuma girmama dokoki da al’adun ƙasashen da za su ziyarta.

Da ta kwatanta mahajjatan a matsayin jakadun Najeriya Dr. Mariya Mahmoud ta ƙarfafa su da su nuna kyawawan dabi’un ƙasar ta hanyar halayensu da mu’amalarsu musamman ta hanyar inganta zaman lafiya haƙuri kishin ƙasa da girmama juna.

Ta kuma yi kira gare su da su yi amfani da wannan damar ta ruhaniya yadda ya kamata ta hanyar yin tunani a kan koyarwar Kristi da kuma barin abubuwan da suka gani da fuskanta a “Ƙasa Mai Tsarki” su zama abin da zai haifar da canji mai kyau a cikin iyalansu majami’unsu al’ummominsu da kuma ƙasar baki ɗaya. Mahmoud ta bayyana fatan cewa darussan ruhaniya daga aikin hajjin za su ƙarfafa jajircewar mahalarta na zama wakilan zaman lafiya sulhu da ci gaban ƙasa.

Ta kuma nanata alƙawarin FCTA na tallafawa shirye-shiryen da ke haɓaka ci gaban ruhaniya, zaman lafiya tare da zama ɗan ƙasa mai alhaki, yayin da take yi wa mahajjata fatan samun kwarewa mai cike da zaman lafiya mai amfani da kuma gamsarwa ta ruhaniya.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button