Afirka

Sama Da Mutane 7,000 Ne Suka Bar Gidajensu Sakamakon Sabon Tashin Hankali A Mozambique

Sama da mutane 7,000 ne aka tilasta musu barin gidajensu bayan sake barkewar rikici a lardin Cabo Delgado da ke arewacin Mozambique wanda hakan ya kara jefa fargabar jin kai da ta ta’azzara bayan kusan shekaru goma na rikicin masu tsattsauran ra’ayi.

A cewar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) jimillar mutane 7,029 ne suka rasa matsugunansu tsakanin 21 ga Satumba zuwa 27 ga Oktoba 2026 a tsakanin sabbin hare-hare da kuma fargabar tashin hankali daga kungiyoyin masu dauke da makamai wadanda ba na gwamnati ba.

Mata da yara sun kai kusan kashi 80 cikin 100 na wadanda suka rasa matsugunansu wanda hakan ke nuna tasirin da rikicin ke yi ga al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali.

Shugabar Ofishin Jakadancin IOM a Mozambique Dana Graber Ladek ta ce sabon rikicin na sanya matsin lamba ga al’ummomin da suka riga suka karbi iyalan da suka rasa matsugunansu sakamakon shekaru na tashin hankali.

“Waɗannan al’ummomi suna buƙatar taimako da abinci matsuguni da kiwon lafiya. Ba tare da tallafi kan lokaci ba rayuwa za ta iya yin wahala ga iyalan da suka rasa matsugunansu da kuma mutanen da ke karbar Bakuncinsu” in ji ta.

Hukumar ta lura cewa an tilasta wa wasu iyalai barin gidajensu sau da yawa wanda hakan ke kara ta’azzara yanayin rayuwarsu da rauninsu.

Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai mata masu juna biyu tsofaffi nakasassu da yara da aka raba su da iyalansu.

Ya zuwa watan Oktoba na 2026 sama da mutane 205,000 da suka rasa matsugunansu suna zaune a wurare 84 na gudun hijira a faɗin Cabo Delgado inda yara suka fi rabin al’ummar da abin ya shafa.

Lardin ya kasance tsakiyar rikicin tun daga shekarar 2017 lokacin da ‘yan bindiga da ke da alaƙa da ƙungiyar IS suka fara kai hari kan ƙauyuka jami’an tsaro da kayayyakin more rayuwa.

Rikicin ya kashe dubban mutane kuma ya raba ɗaruruwan dubbai da gidajensu wanda ya haifar da shiga tsakani na sojoji daga Mozambique Rwanda da Ƙungiyar Ci Gaban Afirka ta Kudu (SADC).

IOM ta gano abinci a matsayin mafi buƙatar gaggawa a tsakanin sabbin gidaje da aka kora sai kuma matsuguni da kiwon lafiya.

Yawancin iyalai da abin ya shafa a halin yanzu suna dogara ne da al’ummomin da ke karɓar masauki wanda hakan ke ƙara matsin lamba ga ƙarancin albarkatu da muhimman ayyuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button