Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Samu Bayanai Kan Muhimman Batutuwan Taron 81 (UNGA)

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya samu cikakken bayani game da halartar da Najeriya za ta yi a taron Majalisar Dinkin Duniya na Babban Zaure karo na 81 (UNGA) a birnin New York na kasar Amurka.
Ministar Harkokin Waje Bianca Odumegwu-Ojukwu da wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya Jakada Jimoh Ibrahim ne suka gabatar wa Mataimakin Shugaban Kasar bayanan a hukumance game da muhimman abubuwan da kasar ta sa a gaba da kuma tsammanin da ake da shi daga masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan kasa gabanin wannan babban taro na duniya.
Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kafafen Yaɗa Labarai da Sadarwa Mista Stanley Nkwocha ya ce “Najeriya za ta gina matsayinta a taron shugabannin duniya na ƙarshe inda ta yi kira da a yi gyare-gyare sosai ga ƙungiyar duniya don ƙara yawan gudummawarta ga ci gaban ƙasashe masu tasowa.”

Nkwocha ya ce lokacin da aka fara zaman taro na 81 a hukumance Mataimakin Shugaban Ƙasa zai gabatar da saƙon Shugaba Tinubu a wurare daban-daban ciki har da ƙoƙarin Najeriya na samun kujera ta dindindin a Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya.
Ya jaddada cewa Najeriya ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da tattaunawa ta dabarun aiki tare da muhimman masu ruwa da tsaki a wannan taron na duniya.

Haka kuma yayin da yake jawabi wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya Jakada Jimoh Ibrahim ya ce“shirye-shiryen kasar na halartar taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 za su mayar da hankali ne kan zurfafa gyare-gyare a wannan kungiya ta duniya domin tabbatar da samun tasiri mai karfi ga kasashe mambobi tare da sauran manufofi.”
Gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara ya kuma bayyana cewa zai halarci taron domin neman damar kulla kawance a matakin duniya da zai iya jawo karin saka hannun jari a jihar.

Gwamna Fubara ya nuna kwarin gwiwar cewa dumbin albarkatun man fetur da iskar gas na Jihar Rivers za su samar da damar gudanar da tattaunawa mai ma’ana tare da masu son saka hannun jari a yayin taron.
Gwamnonin sun bayyana cewa manufar halartar taron ita ce yin amfani da wannan dandamali na kasa da kasa wajen tallata jihohinsu da jawo masu saka hannun jari da kuma samar da sabbin damammakin tattalin arziki ga al’ummominsu.


Ladan Nasidi.



