Sarkin Moroko Mohammed Na Shida Ya Nada Mace Ta Farko Da Za Ta jagoranci Gwamnatin Kasar

Sarkin Moroko Mohammed na shida ya nada mambobin sabuwar gwamnatin kasar a hukumance. A karon farko a tarihin kasar mace ce za ta jagoranci gwamnatin a matsayin Firayim Minista wato Fatima Ezzahra El Mansouri.
Jam’iyyarta mai ra’ayin tsakiya-dama wato ‘Authenticity and Modernity Party’ (PAM) ita ce ta lashe zaben watan Satumba kuma ta kulla kawance da jam’iyyar ‘Istiqlal’ mai ra’ayin dama tare da wasu kananan jam’iyyu biyu masu ra’ayin hagu.
A dunkule suna da kujeru 210 cikin kujeru 395 da ke majalisar dokokin kasar.
KARANTA KUMA: Jam’iyyar PAM Ta Moroko Ta Kafa Gwamnatin Kawance Ta Jam’iyyu hudu
An ci gaba da rike ministoci 13 daga cikin ministoci 31 na gwamnatin da ta gabata a cikin sabuwar majalisar zartarwar ciki har da Nasser Bourita a matsayin Ministan Harkokin Waje da Abdelouafi Laftit a matsayin Ministan Harkokin Cikin Gida.
Fouzi Lekjaa wanda sabon shiga ne a jam’iyyar PAM kuma ya kasance ministan kasafin kudi a gwamnatin da ke barin gado sannan aka fi sani a matsayin shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Moroko an daukaka shi zuwa matsayin Ministan Tattalin Arziki.
Sabuwar gwamnatin ta kunshi mata bakwai har da Firayim Ministar wanda hakan ya yi daidai da yawan matan da ke cikin gwamnatin da ta gabata.
Bayan ganawa da Sarkin El Mansouri ta bayyana cewa gwamnatin za ta aiwatar da “tsare-tsare masu zurfi da buri wadanda za su iya biyan bukatun ‘yan kasa.”
Zaben watan Satumba wanda ya samu karancin fitowar masu kada kuri’a mafi kankanta a cikin kusan shekaru 20 ya gudana ne a yayin da ake nuna damuwa game da tsadar rayuwa rashin aikin yi da rashin daidaito a tsakanin al’umma.
Sabuwar gwamnatin za ta fuskanci kalubalen magance wadannan matsaloli, yayin da take shirye-shiryen karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2030 wadda za a gudanar tare da kasashen Spain da Portugal.



