Afirka Ta Zarce Turai Wajen Yawan Mabiya Katolika

A cewar sabbin alkaluman da Vatican ta fitar Afirka ta zarce Turai a matsayin nahiyar da ke da mafi yawan mabiya Katolika a duniya inda Afirka ke da kashi 20.3 na dukkan Katolikan duniya yayin da Turai ke da kashi 20.2.
Alkaluman wadanda hukumar labarai ta Vatican ta tattara kuma ta fitar a ranar Juma’a sun nuna cewa yawan mabiya Katolika a duniya ya kai biliyan 1.422 a watan Yunin 2024 wanda ya yi daidai da kashi 17.8 na yawan al’ummar duniya baki daya.
Rahoton ya nuna karuwar kashi 0.1 a yawan mabiya Katolika a duniya idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Nahiyoyin Amurka (Arewa da Kudu) ne ke da mafi yawan mabiya Katolika inda suka kai kashi 47.7 sai Afirka da kashi 20.3 Turai da kashi 20.2 Asiya da kashi 11 sannan Oceania da kashi 0.8.



