Siyasa

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Isa Jihar Ekiti Domin Halartar Bikin Rantsar Da Gwamna Oyebanji

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa Ado Ekiti babban birnin jihar Ekiti domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da Gwamna Biodun Oyebanji.

Mataimakin Shugaban ya isa Filin Jiragen Sama na Kasa da Kasa na Ekiti da misalin karfe 10:15 na agogon GMT inda Gwamna Oyebanji da wasu manyan jami’ai suka tarbe shi.

KARANTA KUMA:http://Bikin Rantsar da Gwamna Oyebanji na Wa’adi na Biyu ya Gudana a Ekiti

Oyebanji na fara wa’adinsa na biyu a jere wanda zai dauki tsawon shekaru hudu biyo bayan sake zaben sa a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 20 ga watan Yunin 2026.

A cewar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu kuri’u 319,224 inda ya doke babban abokin hamayyarsa Oluwole Oluyede na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri’u 40,543.

An fara rantsar da Oyebanji a karon farko a ranar 16 ga watan Oktoban 2022 kuma yanzu haka yana fara wani sabon wa’adi na shekaru hudu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button