Duniya

Yemen: Harin Makami Mai linzami Na ‘Yan Houthi Ya Kashe Masu Gadi Biyu A Fada

A ranar Alhamis ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun harba makamai masu linzami guda biyar zuwa harabar fadar shugaban kasa da ke birnin Aden a kudancin kasar lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro biyu a cewar jami’an gwamnati.

Ministan yada labarai na Yemen Moammar al-Eryani ya bayyana cewa firaministan kasar da ministocin gwamnatin da ke cikin harabar fadar shugaban kasa ta Maashiq ba su ji rauni ba sakamakon harin.

Jami’an gwamnati biyu sun tabbatar wa manema labarai faruwar mutuwar mutanen.

KARANTA KUMA: Iran ta harba makamai masu linzami zuwa wani sansani da Amurka ke amfani da shi a Jordan

Kamfanin dillancin labarai na Saba wanda ke karkashin ikon ‘yan tawayen Houthi ya ambato wani jami’in soja yana cewa kungiyar ta kai hari ne kan hedkwatar ayyukan soja da jami’an Saudiyya ke gudanarwa a cikin harabar tare da kai hari kan ma’ajiyar makamai.

Kakakin rundunar sojan kungiyar Yahya Saree ya ce harin da aka kai kan abin da ya kira hedkwatar ayyukan sojan Saudiyya a Aden. wani bangare ne na manufar da ‘yan Houthi suka ayyana ta “kai hari kan tarin karfin sojan Saudiyya a duk inda suke”.

Harin ya nuna ci gaba da tashin hankali tsakanin kungiyar Houthi wacce ke da alaka da Iran  da kuma kasar Saudiyya wacce ta taka rawar gani a rikicin kasar Yemen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button