Najeriya

Gwamnonin Yankin Arewa Ta Tsakiya Sun Goyi Bayan Shirin Shugaba Tinubu Na Sake Tsayawa Takara A 2027

Gwamnonin yankin Arewa ta Tsakiya sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sake samun wa’adin mulki na biyu yayin babban taron jam’iyyar APC da aka gudanar a filin Lafia Square da ke jihar Nasarawa.

A jawabinsa na maraba Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana cewa jihar za ta goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a babban zaben shekarar 2027.

Sule ya nuna kwarin gwiwa kan nasarar da jam’iyyar za ta iya samu a zabe tare da sake jaddada aniyar jihar Nasarawa na ci gaba da goyon bayan APC da ‘yan takararta.

Gwamnonin jihohin Benue Plateau Kwara Kogi Niger da Nasarawa suma sun bayyana goyon bayansu ga yunkurin Tinubu na sake tsayawa takara inda suka yi nuni da sauye-sauyen da aka samu a fannin tattalin arziki da sauran bangarori a karkashin gwamnatinsa.

Da take jawabi a wajen taron Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana kwarin gwiwar cewa matsalolin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta za su ragu tare da fatan samun ingantacciyar rayuwa idan Shugaban ya samu wa’adin mulki na biyu.

Ta yi karin haske kan wasu shirye-shiryen gwamnatin a fannonin kiwon lafiya gina hanyoyi da ilimi ciki har da shirin bayar da rancen kudi ga dalibai da aka tsara domin bai wa karin dalibai damar samun ilimi mai zurfi.

Uwargidan Shugaban Kasa ta bayyana cewa samun wa’adi na biyu ga Tinubu zai ba da damar ci gaba da aiwatar da shirin gwamnati na  ”Sabon Fatan Rayuwa’‘ tare da magance wasu daga cikin kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Wannan jawabi nata na cikin kokarin jam’iyyar APC na tara goyon baya ga Shugaban Kasa da sauran ‘yan takarar jam’iyyar gabanin babban zaben shekarar 2027.

Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyya masu ruwa da tsaki, magoya baya, da kuma abokan huldar siyasa daga sassan yankin Arewa ta Tsakiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button