NYSC Ta Amince Da Karin Kasafin Kudin Abinci Ga Masu Yi Wa Kasa Hidima.

Gwamnatin Najeriya ta amince da karin kudin ciyarwa ga matasan da ke shirin gudanar da hidimar kasa (NYSC) yayin zaman horon shiga shirin a matsayin wani bangare na kokarin inganta jin dadinsu.
Daraktan Janar na hukumar NYSC Birgediya Janar Olakunle Nafiu ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da matasan da ke shirin gudanar da hidimar kasa na rukunin ‘Batch C Stream One’ a sansanin horo na jihar Kuros Riba da ke Obubra a yankin Kudu-maso-Kudancin Najeriya.
Ya bayyana cewa Ofishin Tsara Kasafin Kudi na sane da wannan karin inda ya kara da cewa ana sa ran fara aiwatar da karin a shekara mai zuwa.

KARANTA KUMA: Hukumar NYSC Ta Sanar Da Jadawalin Rukunin C Na Shekarar 2026
Nafiu ya bukaci membobin kungiyar da su yi amfani da hankali su guji salon rayuwa mai cike da alfahari da kuma gina dabi’ar adana kuɗi.
Ya yaba da juriya da jajircewar matasan Najeriya wajen yin hidimar ƙasa.
Darakta Janar ya kuma shawarci membobin kungiyar da su fifita tsaronsu yayin tafiya yana mai kira gare su da su daina tafiyarsu kafin ƙarfe 6 na yamma su ci gaba da washegari idan ya cancanta.
“Kada ku yi barci a wuraren jama’a ko a wuraren cika mai da yawa domin mutane za su gane ku cikin sauƙi” ya yi gargaɗi.
Ya shawarce su da su nemi taimako daga hukumomin tsaro idan ya zama dole.
“Ku je barikokin soja barikokin ‘yan sanda wuraren DSS ku kira layin NYSC” in ji shi.

Nafiu ya bayyana cewa za a kara kaimi wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin inganta da kuma gyara kayan aiki da gine-gine a sansanin horarwa na Obubra.
Ya kuma bukaci matasan da ke shirin bautar kasa su koyi dabarun aiki na zahiri wadanda za su kara darajar takardun shaidar kammala aikin nasu tare da inganta makomarsu.
“Ku koyi abin da zai amfane ku. Ku koyi sana’ar kwalliya da gyaran jiki ku koyi yadda ake daure dankwali da sauran su” in ji shi.
Tun da farko mai kula da harkokin NYSC a jihar Kuros Riba Mrs. Adejoke Oyenuga ta bayyana ziyarar darakta-janar din a matsayin shaida ta jajircewarsa wajen kula da jin dadin matasan da ke bautar kasar.
Ta bayyana cewa matasa masu bautar kasa 1,064 ne suka yi rajista a sansanin inda ta kara da cewa sun saba da tsarin rayuwa mai tsauri na sansanin.



