Jihar Oyo Ta Fadada Shirin Bayar Da Tallafin Karatu Ga Daliban Shekarar Karshe Ga Mutane 5,000

Gwamnatin Jihar Oyo ta kara yawan daliban da ke shekarar karshe da ke cin gajiyar shirin tallafin karatu (bursary) daga 2,600 zuwa kusan 5,000.
Kungiyar Daliban Jihar Oyo ta Kasa (FOSSU) ce ta bayyana hakan a birnin Ibadan inda ta yaba wa gwamnati kan fadada shirin domin ya shafi karin daliban jihar da ke karatu a manyan makarantun gwamnati a fadin Najeriya.
Shugaban kungiyar na kasa Ahmed Mufutau ya bayyana cewa daliban da ke shekarar karshe na fuskantar matsin lamba na kudi saboda ayyukan bincike ayyukan karatu tsarin kammala karatu (clearance) da sauran kudade masu alaka da kammala karatunsu.
Ya bayyana cewa a karkashin shirin na shekarar 2026 daliban shekarar karshe na fannin likitanci (Clinical) da na fannin sararin samaniya da sufurin jiragen sama (Aeronautics and Aviation) za su samu Naira 500,000 kowannensu daliban digiri na farko a jami’a za su samu Naira 200,000 daliban HND za su samu Naira 150,000 yayin da daliban shekarar karshe na shirin NCE za su samu Naira 100,000.
KARANTA KUMA:http://Mace ta Farko da ta Zama Jami’ar Kula da Kudi (Bursar) a Jami’ar Ibadan ta Karbi Ofis
Mufutau ya yaba da matakin hada daliban kwalejojin horar da malamai (Colleges of Education) a cikin shirin yana mai nuna cewa ‘yan asalin jihar Oyo da ke karatu a Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya (Nigerian Law School) sun kasance suna karbar Naira 500,000 duk shekara a karkashin shirin tallafin jihar tsawon shekaru shida a jere.
Ya yi kira ga daliban da suka cika sharuddan shirin da su shirya takardunsu kafin bude shafin yanar gizo na shirin a ranar 12 ga watan Oktoba inda za a rufe rajistar a ranar 1 ga watan Nuwamba.
Kungiyar daliban ta kuma yi gargadi ga masu neman tallafin game da shafukan yanar gizo na bogi da ake amfani da su wajen zamba tare da ba su shawarar dogaro da hanyoyin sadarwa na gwamnati wajen samun bayanai.
A yayin taron manema labarai kungiyar FOSSU ta bayyana goyon bayanta ga kudirin Gwamna Seyi Makinde na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben gama-gari na shekarar 2027.
Mufutau ya ce kungiyar za ta hada karfi da karfe wajen neman goyon baya ga gwamnan yana mai nuni da nasarorin da gwamnatin Makinde ta samu a fannin ilimi da kuma jin dadin dalibai.
Babban Mataimakin Musamman ga Gwamna kan Harkokin Dalibai Victor Olojede, ya kare manufofin gwamnati a fannin ilimi wadanda suka hada da soke kudin makarantar sakandare ta gwamnati na Naira 3,000 daukar malamai aiki rarraba kayan karatu da kuma kokarin mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta zuwa aji.
Ana sa ran shirin tallafin kudi na shekarar 2026 zai samar da tallafin kudi ga dubban daliban da ke shekarar karshe ta karatu yayin da suke kammala digirinsu na farko.



