Kasuwanci

Majalisa Ta Yaba Da Nasarar Kaddamar Da Masana’antar Sukari Ta Oyo

Hukumar Kula da Ci gaban Masana’antar Sukari ta Kasa (NSDC) ta taya kamfanin Oyo Sugar and Derivatives Industries Limited (OSDL) murna bisa kaiwa matakin kaddamarwa da gwajin aiki na masana’antar sukari da ke Iseyin a Jihar Oyo kudu maso yammacin Najeriya.

Babban Sakataren Hukumar Mista Kamar Bakrin ya bayyana cewa wannan muhimmin ci gaba shi ne sakamakon goyon bayan da NSDC ta bayar na tsawon fiye da shekaru goma ta fuskar kudade fasaha da tsare-tsare ga wannan aiki.

A cewarsa wannan sabuwar masana’antar sukari mai karfin sarrafa tan 300 a kowace rana (TCD) wacce aka gina karkashin Shirin Kasa na Inganta Masana’antar Sukari (NSMP) na daya daga cikin sabbin masana’antun sukari kalilan da suka samo asali daga Shirin Hada Harkokin Noma da Masana’antu (Backward Integration Programme) na wannan shiri na kasa.

Mista Bakrin ya yaba wa wadanda suka kaddamar da aikin da kuma al’ummomin manoma na Iseyin bisa yadda suka mayar da shirin daga aikin hadin gwiwar noma zuwa masana’anta mai cikakken aiki.

KARANTA KUMA: http://Jihar Oyo da CGIAR sun hada gwiwa don inganta sarkar darajar rogo da koko

Ya bayyana cewa Hukumar ta dauki nauyin sayen babban injin sarrafa sukari na masana’antar mai karfin tan 300 a rana kan kudi kimanin Naira biliyan 1.64.

Ya kara da cewa yayin da aikin ke ci gaba, NSDC ta samar da karin kudade don bunkasa noman rake da kuma tallafawa ayyukan masana’antar wanda hakan ya sa jimillar kudaden da ta saka a aikin ya kai kimanin Naira biliyan 2.2.

Hukumar ta kuma bayyana cewa Gwamnatin Jihar Oyo ta ba da gudummawar kudi kimanin Naira miliyan 850 a matsayin hannun jari don kammala sauran ayyukan da suka rage a masana’antar.

Mista Bakrin ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga jajircewa da ci gaba da goyon baya daga NSDC Gwamnatin Jihar Oyo da kuma wadanda suka kaddamar da aikin.

“Kasancewar wannan masana’anta a shirye take yanzu don kaddamarwa sakamakon jajircewa ne da ci gaba da goyon baya daga Hukumar Gwamnatin Jihar Oyo da kuma wadanda suka kaddamar da aikin da kansu. Aikinmu bai kare a nan ba. NSDC za ta ci gaba da sa ido da bayar da tallafi yayin da OSDL ke shiga matakin cikakken samar da sukari don kasuwanci kuma muna sa ran wannan aiki zai zama shaida cewa za a iya gina bangaren sukari na Najeriya ta hanyar amfani da raken da ake nomawa a cikin gida” in ji Babban Sakataren.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button