Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Isa Kasar Habasha Don Taron Shugabancin Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya isa birnin Adis Ababa na kasar Habasha a matsayin shugaban tawagar Najeriya a taron musanyar shugabannin samar da abinci mai gina jiki ta Najeriya da Habasha da za a yi daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoban 2026.
Yayin da ya isa birnin Addis Ababa, ya samu tarba daga jakadan Najeriya a Habasha kuma wakilin dindindin a kungiyar Tarayyar Afirka, Ambasada Nasir Aminu; Minista a ma’aikatar, Nura Aliyu; Babban mai ba da shawara, Mista Onovo Emmanuel Isaac; Hafsan Tsaro, Wing Kwamanda Gabriel Batubo, da wasu manyan jami’an gwamnatin Habasha.


Mataimakin Firayim Ministan Habasha, Temesgen Tiruneh—wanda ke jagorantar dabarun kasar na bangarori daban-daban don inganta abinci mai gina jiki—ya gayyace shi zuwa taron ‘Pearl Exchange Forum’.
KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya tashi daga Abuja zuwa Addis Ababa


Mataimakin Shugaban Kasar yana tare da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi.
Har ila yau, cikin tawagar akwai Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu; takwaransa na Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Abinci, Abubakar Kyari; da kuma Darakta-Janar na Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar.

Mataimakin Shugaban Kasa zai dawo Abuja bayan kammala taron a Addis Ababa.
Aisha.Yahaya, Lagos



