Super Eagles Sun Yi Gwagwarmayar Dawo Da Kwallaye Har Suka Tashi Kunnen Doki 3-3 Ra Rasha A Wasan Sada Zumunta.

Najeriya ta dawo daga rashin ci da kwallaye biyu ta kuma tashi kunnen doki 3-3 da Rasha a wasan sada zumunta na kasa da kasa da aka buga a Novgorod ranar Talata da ta gabata.
Kungiyar Super Eagles, wacce ke neman fansar rashin nasarar da ta sha a hannun Guinea-Bissau da ci 3-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2027 a ranar Juma’ar da ta gabata, ta tsinci kanta a baya bayan da ta fara cin kwallo.
Kelechi Iheanacho ne ya fara zura kwallo a ragar Rasha ta hanyar harbi daga bakin yankin bugun fenariti, inda ya bai wa tawagar Eric Chelle damar jagoranci da ci 1-0.
Rasha ta mayar da martani ta hannun Lechi Sadulaev, wanda ya samu damar buga kwallo shi kadai a cikin yankin bugun fenariti kafin ya zura ta a raga, lamarin da ya sa aka tashi 1-1.
Daga nan sai Matvey Kislyak ya kara kwallo ta biyu ga Rasha jim kadan kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda ya bai wa masu masaukin bakin damar jagoranci da ci 2-1 a lokacin hutun.
Karanta kuma: Super Eagles sun fara atisaye gabanin wasan sada zumunta da Rasha
Najeriya ta sha kashi mai tsanani a hannun Guinea-Bissau Rasha ta kara yawan kwallayenta bayan an dawo daga hutun rabin lokaci lokacin da Aleksei Miranchuk ya sa aka tashi 3-1.
Najeriya ta rage tazarar kwallayen ta hannun Edokpolor, wanda ya zura kwallo daya ta sa aka tashi 3-2.
Super Eagles sun ci gaba da kokarin neman kwallon da za ta daidaita sakamakon wasan, kuma sun samu nasara a karshen wasan lokacin da Akor Adams ya zura kwallo ta sa aka tashi 3-3.
Wannan sakamako ya kawo karshen jerin nasarorin da Rasha ke samu a wannan lokacin na wasannin kasa da kasa, bayan da ta doke Iran da Namibia tare da zura kwallaye takwas a dukkan wasannin biyu.
Jerin ‘yan wasan Najeriya da suka fara wasan sun hada da Stanley Nwabali; Samuel James, Emmanuel Fernandez, Benjamin Frederick, Kenneth Igboke; Raphael Onyedika, Chibuzo Nwoko, Stephen Michael; Moses Simon, Akor Adams da Kelechi Iheanacho.
Rasha ta fara wasan da Maxim Maksimenko; Ruslan Litvinov, Danil Denisov, Sergei Osipenko, Danil Krugovoy; Danil Prutsev, Matvey Kislyak, Aleksei Batrakov; Maksim Glushenkov, Konstantin Tyukavin da Lechi Sadulaev.
Wannan sakamakon kunnen doki na 3-3 ya bai wa Najeriya wani abu da za ta tafi da shi daga wasan karshe na wannan lokacin na wasannin kasa da kasa, bayan rashin nasarar da ta sha a hannun Guinea-Bissau.
NP/Aisha.Yahaya, Lagos



