NYSC Ta Sanar Da Jadawalin Rukunin C Na Shekarar 2026

Hukumar Kula da Shirin Yi wa Kasa Hidima ta Matasa (NYSC) ta sanar da cewa za a fara shirin horarwa na rukunin ‘Batch C Stream II’ na shekarar 2026 a ranar Laraba 4 ga watan Nuwamba 2026.
A cikin wata sanarwa da Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta hukumar Caroline Embu ta fitar NYSC ta bayyana cewa za a gudanar da shirin horarwar a dukkan jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja.
KARANTA KUMA: NYSC ta sanar da ranar fara shirin horarwa na rukunin ‘Batch C Stream I’ na shekarar 2026
Bisa ga sanarwar za a gudanar da rajistar mahalarta shirin daga ranar 4 ga watan Nuwamba har zuwa tsakiyar dare na ranar 6 ga watan Nuwamba yayin da aka tsara gudanar da bikin karɓar rantsuwar aiki a ranar Juma’a 6 ga watan Nuwamba.
Ana sa ran shirin horarwar zai kammala a ranar Talata 24 ga watan Nuwamba 2026.



