Gwamnatin Jihar Kogi Ta Yi Jana’izar Tsohon Gwamna Ibrahim Idris.

Gwamnatin Jihar Kogi, dake tsakiyar Najeriya ta gudanar da jana’izar tsohon Gwamnan jihar Ibrahim Idris bisa tsarin da ya dace da matsayinsa na tsohon gwamna a makabartar Gudu dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya a ranar Juma’a.
An binne marigayi Gwamna Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti a Landan bayan fama da rashin lafiya a birnin Abuja kamar yadda ya bayyana a matsayin burinsa kafin rasuwarsa.
Gwamnan Jihar Kogi Ahmed Usman Ododo da tsoffin gwamnonin jihar su biyu Yahaya Bello da Idris Wada na cikin daruruwan masu jajantawa da abokan huldar siyasa na marigayin da suka halarci jana’izar.
An gudanar da sallar jana’izar a Babban Masallacin Abuja bayan sallar Juma’a yayin da aka aiwatar da binne gawar a makabartar Gudu dake Abuja.
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Tsohon gwamnan Jihar Kogi Ibrahim Idris.
Marigayi Gwamna Idris yana da shekaru 77. Ya jagoranci Jihar Kogi daga shekarar 2003 zuwa 2012.

Iyalin sun bayyana godiyarsu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Ahmed Usman Ododo bisa goyon bayan da suka bai wa iyalin Idris da kuma al’ummar jihar Kogi a lokacin zaman makokin.
Marigayi Ibrahim Idris wanda aka fi sani da ‘Ibro’ ya yi fice wajen jagorancin siyasa a jihar musamman ta fuskar ayyukan jin kai ga marasa galihu.
Tsohon Gwamnan Idris ya rasu ne shekaru 15 bayan kammala wa’adinsa a matsayin gwamna na biyu na farar hula a jihar ta Kogi wadda aka fi sani da ‘Confluence State’ inda ya rike mukamin gwamnan jihar mai dumbin albarkatun kasa na tsawon lokaci mafi tsawo tsakanin shekarar 2003 zuwa 2012.

Tsawon lokacin da ya shafe yana rike da mukamin gwamna ya kasance mai cike da jerin shari’o’i da suka samo asali daga kalubalantar zaben da ya kai shi ga mukamin yayin da hakan ya kuma haifar da sauyi a tsarin jadawalin zaben gwamna na jihar.



