Najeriya

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Bukaci Shugabancin Hukumar ECOWAS Da Su Ba Da Fifiko Ga Hadin Kai.

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya yi kira ga sabon shugabancin Hukumar ECOWAS da su ba da fifiko ga hadin kai da dunkulewar yankin domin inganta ci gaban al’umma da tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka.

Mataimakin Shugaban ya bayyana hakan ne a birnin New York yayin da ya karbi bakuncin tawagar Hukumar ECOWAS karkashin jagorancin sabon shugabanta Janar Birame Diop (mai ritaya) a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya na Babban Zaure (UNGA) karo na 81.

Ya ce za a iya cimma wannan ta hanyar gina gadar abota da kuma inganta shirye-shirye da manufofin da za su yi tasiri sosai ga rayuwa da hanyoyin samun abin dogaro da kai na mutane a daukacin yankin.

KARANTA KUMA: Shugaban Hukumar ECOWAS Ya Bayyana Manyan Kalubalen Da Ke Fuskantar Afirka

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bukaci sabon shugabancin da su dauki batun shigar bangaren masu zaman kansu da muhimmanci wajen aiwatar da aikin babbar hanyar Legas-Abidjan.

Ya ce “Baya ga ayyukanka na gudanarwa ya zama dole shugabancinka a hukumar ya yi ƙoƙari na gangan wajen gina kyakkyawar alaƙa da abokantaka a faɗin yankin. Ya kamata ECOWAS ta kasance a sahun gaba wajen mu’amala da sabbin ƙungiyoyin da ke tasowa a yankin kamar su Alliance of Sahel States (AES).

“Ina kira ga ECOWAS a ƙarƙashin shugabancinka da ta zama jagora wajen inganta haɗin kan yankin tare da ƙarfafa alaƙar zumunci da abokantaka a tsakanin al’ummominmu” cewar Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima yayin da yake jawabi ga tawagar.”

Mataimakin Shugaban Kasa ya taya sabon Shugaban Hukumar murna bisa zabensa inda ya yi nuni da cewa ya karbi ragamar shugabanci ne a wani lokaci mai sarkakiya da ke bukatar karin hadin kai da dunkulewar kawuna tsakanin shugabanni da al’ummar yankin.

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya tabbatar wa Janar Diop cewa Najeriya za ta ci gaba da ba da hadin kai da goyon baya inda ya ce “shugabana Shugaba Bola Ahmed Tinubu mutum ne mai mutunci da tsayawa kan manufa wanda zai ci gaba da goyon bayan duk wani yunkuri na inganta sauye-sauyen da ake son kawo wa ECOWAS a matsayin kungiyar yanki da kuma ci gaban yankin baki daya.”

Ya bayyana cewa “Najeriya za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau domin kungiyar ECOWAS ta samu nasara tare da bayar da gagarumar gudunmawa wajen cimma buri da manufofin da wadanda suka kafa kungiyar suka shimfida.”

Janar Diop ya yaba wa Najeriya matuka bisa rawar da ta taka wajen kafa kungiyar ECOWAS da kuma ci gaba da tallafa mata tsawon shekaru tare da sadaukarwar da ta yi domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban yankin Yammacin Afirka duk da kalubalen da ake fuskanta.

Ya bayyana cewa baya ga karuwar damuwa game da rashin tsaro da kuma jinkirin ci gaba a yankin hukumar na fuskantar kalubale na musamman da ke bukatar sa hannun kai-tsaye daga Najeriya a matsayinta na “babban yaya” domin samun nasarar shawo kansu.

Yayin da yake bayyana ECOWAS a matsayin wata kafa ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin wadda ya kamata a rika karfafa gwiwa da kuma ba ta goyon baya a kowane lokaci sabon shugaban ya yi kira ga sauran kasashen yankin da su hada kai da Najeriya domin tabbatar da ci gaba mai dorewa da ya shafi kowa tare da samar da kyakkyawar makoma ga al’ummar yankin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button