DuniyaNajeriya

Jakadan Birtaniya ya Isa Najeriya Domin Fara Gudanar Da Aikinsa.

An nada Pete Vowles a matsayin Babban Kwamishinan Birtaniya a Najeriya kuma ya isa Abuja domin fara gudanar da aikinsa na shugabantar tawagar diflomasiyyar Birtaniya a kasar.

Ofishin Babban Kwamishinan Birtaniya da ke Abuja ne ya sanar da isowarsa ta cikin wata sanarwa.

Vowles zai karbi ragamar aikin ne daga hannun Dr. Richard Montgomery wanda ya rike mukamin Babban Kwamishinan Birtaniya a Najeriya a baya.

KARANTA KUMA: http://Shugaba Tinubu Ya Karbi Babban Kwamishinan Birtaniya Mai Shirin Barin Mukaminsa.

Da yake jawabi a lokacin isowarsa Vowles ya ce babban abin da zai fi mayar da hankali a kai shi ne fahimtar Najeriya sosai da kuma zurfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

“Ina matukar farin cikin kasancewa a Najeriya. Babban abin da zan fi mayar da hankali a kai shi ne sauraro da koyo  yin tafiya saduwa da mutane da kuma nutsar da kaina a cikin wannan kasa mai ban mamaki al’adunta da kuzarinta” cewar Vowles.

Ya bayyana dangantakar da ke tsakanin Burtaniya da Najeriya a matsayin kawance mai zurfi da dorewa wanda aka gina bisa ga kyakkyawar alaƙa tsakanin mutane.

“Birtaniya da Najeriya suna da kyakkyawar alaƙa mai dorewa wadda aka gina a sama da komai akan alaƙar da ke tsakanin mutanenmu” in ji shi.

Vowles ya ce yana fatan yin mu’amala da abokan hulɗa a faɗin Najeriya da kuma gano sabbin damammaki na haɗin gwiwa.

“Ina fatan gano Najeriya da kaina da kuma yin aiki tare da abokan hulɗa a faɗin ƙasar don gina wannan alaƙar da kuma ganin abin da za mu iya cimmawa tare” in ji shi.

Jami’in diflomasiyyar ya kawo ƙwarewa mai yawa a fannin diflomasiyya da ci gaban ƙasashen duniya ga wannan matsayi.

Kafin naɗa shi a Najeriya ya yi aiki a matsayin Jakadan Burtaniya a Zimbabwe. Ya kuma rike mukamai da dama na shugabanci a Ofishin Harkokin Wajen Burtaniya  da Ofishin raya kasa kuma a baya ya yi aiki a matsayin Jakadan Myanmar.

Vowles ya gudanar da ayyukan diflomasiyya da ci gaba a fadin Afirka da Asiya ciki har da mukamai a Bangladesh Indiya Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Kenya.

Gwamnatin Burtaniya ta sanar da nadinsa a matsayin sabon Kwamishinan Burtaniya a Najeriya a ranar 16 ga Yuni 2026.

Zuwarsa ta zo ne yayin da kasashen biyu ke ci gaba da karfafa hadin gwiwa a fannin diflomasiyya cinik ci gaba da kuma huldar da ke tsakanin mutane.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button