Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Taya Gwamnan Kwara Murnar Karɓar Sarautar Gargajiya A Ilori

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq murnar nada shi da kuma sanya masa rawani a matsayin Sardaunan Ilorin.

Shugaba Tinubu ya bukace shi da ya karbi wannan lakabi mai matukar muhimmanci a fannin al’ada da ba wai kawai a matsayin abin girmamawa ba har ma a matsayin kira zuwa ga kara himma wajen hidima da kuma daukar nauyi.

 

Sarkin Ilorin na 11 kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara Mai Martaba Alhaji Dr. Ibrahim Kolapo Sulu-Gambari ne zai nada Gwamna AbdulRazaq wannan sarauta a birnin Ilorin a ranar Laraba, 16 ga watan Satumba.

 

Karanta kuma:

A cikin sakon taya murna da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya fitar Shugaba Tinubu ya yaba wa Sarkin bisa karrama Gwamna AbdulRazaq da wannan mukami mai daraja; gwamnan wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Yankuna ta Afirka (Forum of Regions of Africa).

Shugaban ya bayyana wannan karramawa a matsayin matakin da ya dace wajen amincewa da irin jagoranci, hidimar jama’a, da gudummawar da Gwamnan ya bayar wajen ci gaban Jihar Kwara musamman kokarinsa na inganta ci gaba mai dorewa da ya shafi kowa da hadin kan al’umma da kuma jin dadin jama’a.

Haka kuma ya yaba wa Sarkin bisa ci gaba da gudanar da muhimmiyar rawar da masarautun gargajiya ke takawa wajen samar da zaman lafiya da hadin kai tare da goyon bayan tsarin mulkin dimokuradiyya da ci gaba mai dorewa.

Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Gwamna AbdulRazaq zai yi amfani da gogewarshi da kwarewarshi a fannin jagoranci da kuma kyakkyawan kudirinsa wajen kare muradun al’ummar Jihar Kwara da kuma bayar da gudummawa ga ci gaba da hadin kan Najeriya.

Shugaban ya yi wa Gwamnan fatan samun nasara da hikima da karfi da kuma koshin lafiya yayin da yake karbar nauyin mukamin Sardaunan Ilorin tare da fatan cewa wannan karramawa za ta kara zaburar da shi wajen zurfafa hidimarsa ga al’umma da kasa baki daya.

 

 

Ladan Nasidi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button