Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Ta Yi Rahoton Sama Da Mutane 7,000 Suka kamu da cutar Ebola.

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo (DRC) ta samu sama da mutane 7,000 da suka kamu da cutar Ebola a wannan sabon bullar cutar inda aka bayar da rahoton mutuwar mutane 3,398 tun lokacin da annobar ta fara a watan Mayu.
Kididdigar da hukumomin Congo suka fitar ta nuna cewa an samu mutane 7,022 da suka kamu da cutar yayin da mutane 1,671 suka warke daga cutar.
Sai dai gwamnati ta ce yaduwar kwayar cutar na iya zama ta kai kololuwarta, duk da cewa an tabbatar da bullar Ebola a wani yanki na bakwai a farkon wannan makon.
Kakakin gwamnati Patrick Muyaya, ya ce an kai kololuwar yaduwar cutar ne a mako na uku na watan Agusta kuma alamomi sun nuna raguwar sabbin masu kamuwa da cutar.
Muyaya ya ce yankuna 10 cikin yankuna 61 na kiwon lafiya da annobar ta shafa ba su samu rahoton sabbin masu kamuwa da cutar ba tsawon akalla kwanaki 21.
KARANTA KUMA:http://Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira da a dauki matakin gaggawa kan Ebola a DRC
Annobar ta fara ne a yankin Ituri da ke arewa maso gabashin DRC kafin ta yadu zuwa wasu yankuna masu nisa da kuma yankunan da rikici ya shafa, inda rashin karfin ikon gwamnati da karancin kayan aikin kiwon lafiya suka kawo cikas ga kokarin shawo kan cutar.
Haka kuma an tabbatar da bullar Ebola a farkon wannan makon a yankin South-Ubangi, wanda ke iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Congo.
Yawancin wadanda suka kamu da cutar suna yankin Ituri ne, inda gano cutar Ebola a tsakanin daliban makaranta bayan komawa makaranta ya haifar da damuwa ga iyaye da ma’aikatan kiwon lafiya.
Matakan Kare Kai
Hukumomin kiwon lafiya da jami’an makaranta sun gabatar da matakan kare kai, wadanda suka hada da wajabta wanke hannu da sabulu da kuma iyakance yawan dalibai a aji zuwa 30.
Jami’an makaranta sun kuma bukaci dalibai su guji taba juna tare da ci gaba da wanke hannu akai-akai.
Ana daukar cutar Ebola ne ta hanyar taba ruwan jikin mutumin da ke dauke da cutar kuma tana iya haifar da tsananin rashin lafiya da mutuwa.
Wannan annoba ta yanzu tana faruwa ne sakamakon nau’in kwayar cutar mai suna Bundibugyo, wadda a halin yanzu ba ta da ingantaccen rigakafi ko takamaiman magani, duk da cewa ana gwada wasu rigakafi da magunguna daban-daban.



