Bakin Haure 5,300 Sun Koma Morocco Daga Ceuta Bisa Radin Kansu.

Gwamnatin Spain ta bayyana cewa fiye da bakin haure 5,300 da suka zauna a yankin Ceuta na Spain da ke Arewacin Afirka bayan kwararar mutane da aka gani a watan Yuli sun koma Morocco da kansu.
Ministan kula da harkokin bakin haure, Angel Victor Torres, ya ce bakin haure 5,321 ne suka koma Morocco tun ranar 10 ga watan Agusta, yayin da wasu 90 suka janye bukatar neman mafakar kasa da kasa.
Torres ya kara da cewa ana ci gaba da yin rajistar wasu karin bakin haure kusan 1,000 domin kammala tsarin komawarsu.
Fiye da mutane 70,000 ne suka shiga Ceuta a ranakun 30 da 31 ga watan Yuli a wani yanayi na kwararar mutane da ba a taba ganin irinsa ba, duk da cewa yawancinsu sun koma Morocco cikin ‘yan sa’o’i kadan.
Dubban mutanen da suka rage a yankin sun bi ta tsarin tantancewa domin sanin ko sun cancanci samun mafaka.
Dokar Spain ta haramta korar yara kanana da ba su tare da iyayensu ko masu kula da su ba ta hanyar gaggawa.
Har yanzu akwai sabani kan ainihin adadin bakin hauren da suka rage a Ceuta. Shugaban birnin mai ra’ayin mazan jiya ya yi hasashen cewa akwai bakin haure kusan 13,000 da suka rage, yayin da gwamnatin tarayyar Spain ke ganin adadin ya yi kasa sosai fiye da haka.
Hukumomi na fadada wuraren zama na wucin-gadi domin daukar bakin hauren, tare da shirye-shiryen samar da wuraren da za su iya daukar mutane har 6,000.
Matsalar bakin hauren na kuma kara matsin lamba na siyasa kan Firayim Minista Pedro Sanchez yayin da ake shirin gudanar da zabe a shekara mai zuwa.



