Ukraine Na Shirin Tattaunawa Da Rasha Da Amurka A Watan Oktoba

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Ukraine Kyrylo Budanov ya bayyana cewa kasar na shirin sake fara tattaunawa mai bangarori uku tare da Rasha da Amurka a watan Oktoba.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen wani taro a Kyiv babban birnin kasar Ukraine.
“Muna shiri. A watan Oktoba” in ji Budanov.
KARANTA KUMA: http://Kremlin a shirye take ta sake fara tattaunawar zaman lafiya da Ukraine
Budanov ya yi wannan jawabi ne ‘yan kwanaki bayan da wakilan Amurka Steve Witkoff da Jared Kushner, suka gudanar da tattaunawa a Moscow da Kyiv—ziyarar farko da suka kai wadannan birane biyu cikin watanni da dama.
Bayan ziyarar Witkoff ya bayyana cewa “sun yi maraba da sabon kuzarin da aka samu wajen ci gaba da tattaunawar.”
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya bayyana cewa wakilan sun gabatar da wasu “ra’ayoyi masu kyau da amfani” tare da ba da shawarar cewa Turkiyya Hadaddiyar Daular Larabawa Switzerland ko wasu kasashen na iya karbar bakuncin sabuwar tattaunawar mai bangarori uku.
An gudanar da irin wannan tattaunawa ta karshe a Geneva a watan Fabrairu amma daga baya tattaunawar ta tsaya cak yayin da hankalin Washington ya koma kan rikicin da ke tsakaninta da Iran.
Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya bayyana cewa Moscow ba ta rufe kofa ga yiwuwar sake fara tattaunawar zaman lafiya ba amma ya ce har yanzu ba a kai ga tantance lokaci ko wurin da za a gudanar da tattaunawar ba.



