Kakakin Majalisa Ya Yi Ta’aziyyar Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Bamanga Tukur.

Kakakin Majalisar Wakilai Abbas Tajudeen ya bayyana rasuwar tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Bamanga Tukur a matsayin babban rashi ga bangaren kasuwanci da siyasar Najeriya.
Tukur wanda ya rasu a ranar Asabar, kwana uku kafin cika shekaru 91 da haihuwarsa ya kasance hamshakin dan kasuwa dattijo mai daraja kuma daya daga cikin manyan ‘yan siyasa na Arewacin Najeriya.
Abbas ya bayyana sakon ta’aziyyarsa ta hannun Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai Musa Abdullahi Krishi inda ya kwatanta Tukur a matsayin dattijo wanda gudummawarsa za ta ci gaba da kasancewa a rubuce a tarihin Najeriya har abada.
KARANTA KUMA:http://Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa Bamanga Tukur ya rasu yana da shekaru 90
Kakakin majalisar ya jaddada gudummawar da Tukur ya bayar a fannonin gudanar da harkokin gwamnati shugabanci masana’antu siyasa da jagorancin kasuwanci a matakin nahiyar Afirka tare da nuna jajircewarsa wajen addinin Musulunci da ayyukan jin kai.
Ya bayyana cewa Tukur a lokacin da yake Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa dimokuradiyyar Najeriya da kuma inganta kyawawan dabi’un siyasa.
Abbas ya mika ta’aziyyarsa ga iyalin Tukur al’ummarsa abokan huldarsa na kasuwanci da siyasa tare da gwamnatoci da al’ummar jihohin Adamawa da Taraba.
Kakakin majalisar ya yi addu’ar Allah (SWT) Ya gafarta wa Tukur kurakuransa tare da ba shi gidan Aljannar Firdausi.



