‘Yan Gudun Hijirar Yemen 1,400 Ne Suka Isa Djibouti

Ministan Tattalin Arziki da Kudi na Djibouti Ilyas Moussa Dawaleh ya bayyana cewa kimanin ‘yan gudun hijira 1,400 ne suka isa kasar daga Yemen cikin sa’o’i 24.
Dawaleh ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin X a ranar Asabar.
“‘Yan gudun hijira 1,400 ne suka isa Djibouti daga Yemen cikin sa’o’i 24 kacal” in ji shi.
A wani sako daban da ya wallafa a ranar Juma’a ministan ya ce ‘yan gudun hijira 500 ciki har da mata da yara sun isa birnin Obock mai gabar teku bayan an ceto su a teku sakamakon karewar man fetur a kwale-kwalensu yayin da suke ketare mashigar ruwa ta Bab-el-Mandeb.
Birnin Obock wanda ke da nisan kilomita 20 kacal ta ruwa daga gabar tekun Yemen ya kasance wurin da mutanen da ke neman mafaka daga yakin Yemen suka fi so su sauka tsawon shekaru da dama.
Haka kuma ana amfani da mashigar ruwa ta Bab-el-Mandeb ta akasin haka inda ‘yan ci-rani daga yankin Kahon Afirka ke bi ta cikinta zuwa kasashen Gulf yayin tafiyarsu.
Mai kula da ayyukan agaji na kungiyar kula da ‘yan ci-rani ta duniya (IOM) Safiya Ibrahim ta ce mutane masu rauni ciki har da mata da yara sun isa gabar tekun Obock kuma ana sa ran karin mutane a kwanaki masu zuwa.
A ranar Asabar, kungiyar IOM ta bayyana cewa mutane 76,000 ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Yemen tun watan Yuli inda adadin ya karu sau hudu bayan sake tsanantar fada a yankin.
Djibouti tana karbar bakuncin dubban ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka. Alkaluman hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya na watan Maris na 2026 sun nuna cewa akwai mutane sama da 36,000 da aka yi wa rajista inda mafi yawansu suka fito daga Somaliya Habasha da Yemen.



