Najeriya

Uwar Gidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Shirin Taskar Abinci Na Ƙasa A Yankin Kudu Maso Gabas

Uwargidan Shugaban Kasar Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta kaddamar da shirin Bankin Abinci na Al’umma na Kasa a Jihar Anambra wanda ke da nufin magance matsalar rashin ingantaccen abinci ga yara a yankin Kudu-maso-Gabas.

Tare da wannan kaddamarwa Uwargidan Shugaban Kasar ta kammala shimfida shirin a dukkan yankuna shida na siyasa na kasar.

Da take jawabi a wajen taron Mrs. Tinubu ta ce dole ne a ajiye bambance-bambancen siyasa a gefe domin biyan bukatun ‘yan Najeriya.

Yayin da take jawabi ga mazauna yankin da suka taru a filin Alex Ekwueme domin tarbarta Uwargidan Shugaban Kasar ta bayyana kammala shimfida shirin a dukkan yankunan kasar a matsayin “nasarar cimma manufa” tare da nuna kyakkyawan fata game da makomar yaran Najeriya.

Ta ce kaddamar da shirin a yankin Kudu-maso-Gabas ya kamata ya haifar da sabon sha’awa a dukkan matakai wajen inganta abincin yara a fadin kasar.

KARANTA KUMA: Uwargidan Shugaban Najeriya ta yi Bikin Murnar Cika Shekaru 60 Da VP Shettima Ya Yi

Sanata Tinubu ta yaba wa Gwamnan Jihar Anambra  Farfesa Charles Soludo da matarsa ​​bisa manufofi da shirye-shiryen da suka aiwatar inda ta bayyana su a matsayin shaida ta hangen nesa na ci gaba da gwamnan ke da shi.

Haka kuma  Uwargidan Shugaban Kasar ta kaddamar da Cibiyar Kwarewa ta ICT (ICT Experience Centre) a karkashin shirin ‘Renewed Hope Initiative’ da Asusun Tallafawa Ilimin Manyan Makarantu (TETFund) a Kwalejin Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic) da ke Oko.

Yayin da take tattaunawa da dalibai a daya daga cikin zauren karatu ta bukace su da su binciko hanyoyi masu amfani na yin amfani da fasaha musamman fasahar kere-keren kwakwalwa (AI) domin magance matsalolin al’umma.

Ta kuma karfafa wa daliban gwiwa su shiga kungiyar kare muhalli (Environment Society) tare da samar da hanyoyin magance matsalolin da ke shafar muhalli.

Uwargidan Shugaban Kasar ta ce inganta ilimin zamani na na’ura mai kwakwalwa (digital learning) a Najeriya ta hanyar kaddamar da cibiyoyin kwarewa na ICT na daya daga cikin muhimman abubuwan da shirin ‘Renewed Hope Initiative’ ya sa gaba.

Yayin kaddamar da raba kayan tallafi da gwamnatin Jihar Anambra ta samar ga mutane 5,000, Mrs. Tinubu ta sanar da bayar da tallafin kudi na Naira 100,000 ga kowane mutum domin tallafawa shirin.

Gwamnan Jihar Anambra  Farfesa Charles Soludo ya bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Gwamnatin Jihar Anambra na haifar da ci gaba tare da taimakawa wajen samar da tsarin da ba ya barin kowa a baya. A matsayin nuna godiya ga gudummawar da ta bayar wajen ci gaban kasa da kuma goyon bayan da ta bai wa mijinta Shugaba Bola Tinubu Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Anambra Igwe Chidubem Iweka ya nada Uwargidan Shugaban Kasa sarautar gargajiya ta “Ugoeze of Anambra” wadda ke nufin “Alfaharin Sarki.“

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button