Koriya Ta Arewa Da Rasha Sun Bude Gadar Hanya Ta Farko

Koriya ta Arewa da Rasha sun bude gadar hanya ta farko inda suka nuna karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma samar da sabuwar hanya kai tsaye don cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Gadar mai tsawon kilomita 1 mai layuka biyu ta ratsa kogin Tumen kuma an bude ta ne a wani biki da Firayim Ministan Rasha Mikhail Mishustin da Firayim Ministan Koriya ta Arewa Pak Thae Song suka halarta daga nesa. Motocin da aka yi wa ado da tuta suna daga cikin motocin farko da suka ketare.
Aikin wanda aka tattauna tsawon shekaru da ya fara ne a watan Afrilun bara bayan yarjejeniyar da aka cimma a lokacin ziyarar Shugaba Vladimir Putin a Koriya ta Arewa a shekarar 2024. Kasashen biyu sun riga sun mallaki hanyoyin jiragen sama da na jirgin kasa amma sabuwar gadar ta samar da hanyarsu ta farko ta musamman.
“Na gamsu cewa fadada kayayyakin more rayuwa na sufuri na ketare zai samar da wani gagarumin ci gaba ga ci gaban cinikayya da tattalin arziki da kimiyya da fasaha da al’adu” in ji Mishustin yana mai bayyana dangantakar kasashen biyu a matsayin “a wani babban mataki da ba a taba ganin irinsa ba” da kuma bude gadar a matsayin “wani muhimmin abin tarihi.”
Ya kira tsarin “sabon alama ta abota”.
Gwamnatin Rasha ta ce gadar za ta iya ɗaukar motoci har 300 a rana kuma za ta haɗu da hanyar sadarwa ta tarayya ta Rasha da kuma hanyar sufuri da ke haɗa Vladivostok da St Petersburg. Ana sa ran za a fara jigilar kaya nan take yayin da za a iya ba da izinin zirga-zirgar fasinjoji da zarar gadar ta fara aiki gaba ɗaya daga baya a wannan shekarar.
An gina sabon ginin kusa da Gadar Abokantaka ta yanzu da wacce aka gina tun daga shekarar 1959 an sanya wa sabon ginin suna bayan Yakov Novichenko, wani sojan Soviet wanda Koriya ta Arewa ta yaba da ceton rayuwar Kim Il Sung a shekarar 1946.
Kafofin watsa labaran gwamnatin Koriya ta Arewa sun ce gadar za ta taimaka wajen kara hadin gwiwa a fannin tattalin arziki ciki har da cinikayya yawon bude ido da kuma musayar ra’ayi tsakanin mutane.
Bude gadar ta zo ne yayin da dangantaka tsakanin Moscow da Pyongyang ta kara karfi tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a shekarar 2022. Koriya ta Arewa ta ba da tallafin soja ga Rasha, ciki har da aika sojoji zuwa yankin Kursk a lokacin fada bayan wani hari da Ukraine ta kai a shekarar 2024.Mishustin ya yi magana game da wannan hadin gwiwa, yana yaba wa “jaruman Koriya wadanda, kwanan nan, suka yi fada kafada da kafada da sojojinmu suka kuma kare kasar Rasha”.
Gadar za ta iya kara hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da dabaru yayin da kuma ta gabatar da tambayoyi game da yuwuwar amfani da dabarunta. Lim Eul-chul, farfesa a Jami’ar Kyungnam da ke Koriya ta Kudu ya ce ci gaban ya nuna karuwar dangantakar aiki tsakanin gwamnatocin biyu.
KARANTA KUMA: Koriya ta Arewa da Rasha sun karfafa kawancen dabarun
“Yayin da Koriya ta Arewa ke kokarin kara karfin muradunta da Rasha ta sami hanyar kai tsaye don jigilar kayayyakin soji da harsasai da ma’aikata gami da sojoji saboda yakin da ta dade tana yi a Yukren.”
Saboda haka sabuwar hanyar ketarewa tana da mahimmanci a fannin tattalin arziki da kuma dabarun ci gaba wanda hakan ke bai wa Masko da Pyongyang wata hanya ta fadada hadin gwiwa yayin da kawancensu ke ci gaba da zurfafa.
Reuters/Ladan Nasidi.



