Jam’iyyar PDP Na Jimamin Rasuwar Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa Dan Orbih
Safina Umar Farouk

Shugaban rikon kwarya na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matakin kasa Kabiru Turaki ya bayyana matukar kaduwa da bakin ciki game da rasuwar tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (bangaren Kudu-maso-Kudu) Chief Dan Orbih.
Turaki ya mika sakon ta’aziyyarsa bayan da iyalan Orbih suka sanar da rasuwarsa inda ya bayyana mutuwar tasa a matsayin babban rashi mai zafi ga jam’iyyar PDP.
Ya ce “Marigayi Chief Dan Orbih ya rike mukamai daban-daban a cikin babbar jam’iyyar mu kuma ya bayar da gagarumar gudummawa a kowane daya daga cikin wadannan mukamai. Muna matukar jimamin rasuwarsa.”
“Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi hutun har abada tare da bai wa iyalansa abokansa da abokan aikinsa karfi da juriya domin jure wannan rashi mai zafi.”
Safina Umar Farouk.



