Rushewar Ramin Hakar Zinare Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 82 A Sudan

Akalla mutane 82 ne suka mutu yayin da wasu kimanin 50 suka jikkata bayan rugujewar wani ma’adinan zinare a Jihar Kordofan ta Yamma da ke Sudan inda ake fargabar cewa ma’aikatan hakar ma’adinai da ba a san adadinsu ba sun makale a ƙarƙashin tarkacen.
Tawagar ceto da abokan aikinsu sun yi aiki cikin dare suna amfani da kayan aiki na asali don gano waɗanda abin ya shafa suna dawo da gawawwaki 60 da asubahi sannan wasu 22 kuma a ranar Laraba.
Wani mai kula da yankin ya ce kimanin mutane 50 ne suka ji rauni a rugujewar yayin da har yanzu ba a san adadin mutanen da suka ɓace ba.
Lamarin ya nuna haɗarin da ke tattare da ɓangaren haƙar zinare mara tsari a Sudan inda miliyoyin mutane ke dogaro da ƙananan haƙar ma’adinai don rayuwarsu.
Masu hakar ma’adinai da yawa suna aiki a cikin ramuka marasa ƙarfi tare da ƙarancin kayan aikin tsaro da kayan aiki na asali wanda ke ƙara haɗarin rugujewar ma’adinan da sauran haɗurra.
KU KARANTA KUMA: Rushewar Mahakar Ma’adinan Sudan Ta Kashe Mutane 11 Tare Da Raunata 7
Har ila yau zinare ya zama muhimmiyar hanyar samun kudi ga bangarorin da ke fada da juna a yakin da ake yi a Sudan wanda yanzu ya shiga shekararsa ta hudu.
Ana bayar da rahoton cewa ana fasa-kwaurin yawancin zinaren kasar zuwa kasashen waje ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kokarin ceto na ci gaba da fuskantar kalubale kasancewar ana bukatar manyan na’urori domin isa ga wadanda ka iya kasancewa sun makale yayin da masu aikin ceto ke fafutukar gaggauta aikin a yankin da rikicin ya yi wa mummunan illa.



