Siyasa

Jam’iyyar PDP Ta Amince Da Shirin G-100 Na Kawancen Jam’iyyun Adawa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta amince da shirin da kungiyar G-100 ke jagoranta wanda ke da nufin kulla kawancen jam’iyyun adawa mai karfi domin kalubalantar jam’iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC) a babban zaben shekarar 2027.

Jam’iyyar ta bayyana matsayinta ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa Kwamrad Ini Ememobong ya fitar inda ya bayyana G-100 a matsayin kungiyar fitattun ‘yan siyasa 100 na jam’iyyun adawa da suka kuduri aniyar samar da dandamalin siyasa na hadin gwiwa mai inganci wanda zai bai wa ‘yan Najeriya zabin da ya dace kuma abin dogaro.

PDP ta bayyana cewa matakin nata ya samo asali ne daga damuwa da takaicin da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon tsananin halin kunci na tattalin arziki da rashin tsaro tare da bukatar haduwar karfin siyasa mai inganci domin neman mafita ga kalubalen da kasar ke fuskanta baki daya.

Shugaban Jam’iyyar na Kasa Kabiru Tanimu Turaki ya bayyana cewa shigarsu cikin wannan tsari ya dogara ne kan fatan cewa za a gudanar da shi cikin gaskiya da adalci da kuma yanke hukunci bisa ingantattun bayanai tare da tabbatar da daidaito ga kowa.

 

KARANTA KUMA: Kwamitin Amintattu (BoT) na PDP ya sanar da kawo karshen rikici ya kuma mayar da hankali kan farfado da jam’iyyar

“Shigarmu ta dogara ne kan alkawarin cewa tsarin zai ginu ne bisa ginshikan gaskiya da daidaito da yanke hukunci bisa bayanai da kuma samar da daidaito ga kowa. Duk wani sakamako da ya fito daga tsarin da aka gudanar bisa wadannan kyawawan halaye tabbas zai samar wa ‘yan Najeriya shugabanci mai inganci wanda zai iya rage tsananin talauci da karuwar rashin tsaro a kasar” in ji Turaki.

 

 

Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button